Jirgin Saman Sojin Najeriya Ya Gano Asibitin ’Yan ISWAP a Sambisa, Ya Ragargaje Shi
- Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar gano mafakar 'yan ta'adda, inda ta ragargaji wani asibitinn 'yan ISWAP
- Rundunar to soji ta hallaka 'yan ta'adda da dama dake kwance a asibitin na cikin dajin Sambisa da ya yi kaurin suna
- Rundunar soja ta ce tana samun nasara matuka wajen yakar 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
Jihar Borno - Jirgin sojojin saman Najeriya na Super Tucano ya gano wani asibiti da 'yan ta'addan ISWAP ke jinya tare da iyalansu a dajin Sambisa, ya ragargaji asibitin tsagerun.
A cewar wani rahoton The Nation, asibitin da ke yankin 'Somalia' na dajin Sambisa ya gamu da fushin sojojin Operation Hadin Kai bayan samun cikakkun bayanan sirri.
Rahoton ya kuma shaida cewa, an hallaka 'yan ta'addan da yawa yayin da suke kokarin guduwa.
Harin na Super Tucano ya biyo barin wuta da sojojin Najeriya ke kara yi a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram da ISWAP Daily Nigerian ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso Gabas
Wani rahoto daga majiyar sojoji ya ce, rundunar soji na kara samun nasarar fatattakar 'yan ta'adda a yankin ta sama da kasa duk da sauyin yanayi da ake fuskanta.
Da aka tuntubi Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, AC Edward Gabkwet, ya tabbatar da faruwar farmakin na soja a yankin na jihar Borno.
Ya kuma kara alkawarin cewa, rundunonin sojin Najeriya za su ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Yankin Arewacin Najeriya na yawan samun farmakin 'yan ta'adda, lamarin da ya daidaita al'ummomi da da yankuna a jihohin yankin.
Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu
'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma, Henry Gotip a Jihar Filato
A wani labarin, yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Gotip da sanyin safiyar yau Laraba 7 ga watan Satumba.
Rahoto ya ce an sacea Gotip ne a gidansa dake Kwang a karamar hukumar Jos ta Arewa, rahoton jaridar This Day.
Majiya ta ce, an 'yan bindigan sun yi harbe-harbe don tsorata mazauna yankin kafin yin awon gaba da Gotip.
Asali: Legit.ng