Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Maida Dalibin Likitanci Mai Siyar da Abinci a Jihar Sokoto
- Matashi ya ba da mamaki yayin da ya bude shagon siyar da abinci sanadiyyar yajin aikin da ASUU ke ciki
- Kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta shiga yajin aiki tun farkon shekarar nan, kuma har yanzu dai ba a dawo ba
- Dalibai a Najeriya na mayar da hankali wajen gina sana'a domin rike kai a madadin bata lokacin jiran karshen yajin aikin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Sokoto - Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.
Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.
Dalibin da ya bude shagon siyar da abinci ya ce yajin aikin ASUU ya bashi damar fara sana'a tare da habaka ta cikin kankanin lokaci a birnin Sokoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya shaidawa kamfanin dillacin Najeriya (NAN) cewa:
“Na karbi hayar shago, na dauki ma’aikata takwas domin kula da fannin siyar da shayi, indomie, sayar da kayan sha na kwalba da gwangwani, masa, shinkafa da wake, farfesu da nama da ma fannin POS.
“Muna siyar da farantin abinci daga N200 zuwa sama daidai bukatan kwastoma."
Adadin ma'aikatansa da shagunansa
Ya ce ya kama shagon ne a titin Fodio a tsakiyar birnin na Sokoto, kuma alamu sun nuna kwalliya na biyan kudin sabulu, domin kuwa yana ma da shagon siyar da kayayyakin sanyawa na mata da maza a gefen da dalibai suka fi yawa.
Ya ce yana farin ciki da yadda ya ba matasa aikin yi, kuma ya zuwa yanzu yana da ma'aikata har 10 a shagunan nasa.
Ya kuma bayyana cewa, yanzu dai ya fi karfin tambayar iyayensa kudi, domin yana samun kudaden shigan da ke iya magance masa matsalolin kudi.
Ta yaya ya samu kudin bude shago?
Abin mamaki, ya ce sam bai karbi bashin banki ko wasu mutane ba, kuma bai nemi wani tallafin matasa daga gwamnati ba.
Ya ce, ya fara sana'ar rarraba kaji da kwai tun lokacin da annobar Korona ta bullo, kuma a nan ne ya dan hada kudaden da suka zame masa jarin fara kasuwa.
Kasuwa mai bukatar jama'a ce, don haka ya samu damar sanin jama'a da dama da kuma wuraren cin abinci, inda yake kai kaji da kwai, rahoton Daily Nigerian.
Da yake maganar riba, matashin ya ce:
"Ganin irin ribar da nake kwasa da kuma irin damammaki da na samu, zan ci gaba da wannan kasuwa ko da kuwa bayan na kammala karatu na ne.
"Idan na zama likita, zan kokarin neman aikin da ba zai ci lokaci da yawa ba, saboda a yanzu na fara cire raina kan aikin da za a ke biya na albashi."
Kira ga matasa da gwamnati
A bangare guda, ya shawarci matasa da su kama sana'a kafin dare ya yi musu, domin hakan ne zai iya zame musu silar arziki da za su iya rike kansu.
Hakazalika, ya yi kira ga gwamnatin Buhari da ta duba lamurran malaman jami'a da makomar dalibai domin dinke barakar dake tsakani.
Yajin aikin ASUU: Dalibin aji 2 a jami'a ya koma sayar da shayi a Kano
Ba Usman Abubakar-Rimi kadai ba, wani dalibin aji biyu na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da yajin aiki ASUU ya shafa ya kama wata sana’ar sayar da “Shayi” a garin Dawakin Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano domin kaucewa zaman banza.
Dalibin mai karanta Tarihi da Hulda da Kasashen Duniya wanda ya bayyana sunansa da Yusuf Auwal Barkum, a wata hira da ya yi da Sahelian Times, ya ce ya yi nadamar rashin kama sana’ar tun da farko.
Teburin shayi dai kasuwanci ne na gida inda ake sayar da dafaffiyar taliya, kwai, shayi da burodi, galibi a fili da ke da karamin shago da benci, teburi da kujeru a zagaye dasu.
Asali: Legit.ng