Na Dade Ashe Yaudarar Kaina Nake Cewa Zan Iya Magance Matsalar Yajin Aiki: Ministan Ilimi

Na Dade Ashe Yaudarar Kaina Nake Cewa Zan Iya Magance Matsalar Yajin Aiki: Ministan Ilimi

  • An fara zaman shugabannin jami'o'in Najeriya da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a Abuja
  • Daga fara zama, Ministan Ilimi ya bayyana cewa tsawon makonni biyu yanzu yana cikin bakin ciki da takaici
  • Yau kwana ta 204 kenan da daliban jami'o'in Najeriya ke zaman gida sakamakon yajin aikin da malamansu suka shiga

Abuja - Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a ranar Talata ya bayyana cewa ya kasance cikin bakin ciki da takaici kan rikicin yajin aikin Malaman jami'a da yaki ci, yaki cinyewa.

Adamu Adamu ya bayyana hakan lokacin zama da shugabannin jami'o'in gwamnatin tarayya a ofishin NUC dake Maitama Abuja, rahoton Punch.

A cewarsa, ashe ya dade yana yaudarar kansa cewa zai iya kawo karshen matsalar yajin aiki bangaren Ilimi.

Yace:

"Tsawon makonni biyu da suka gabata na shiga cikin bakin takaici da bakin ciki. Na kasance ina yaudarar kaina cewa idan akwai Ikhlasi da gaskiya, zan iya kawo karshen yajin aiki a bangaren Ilimi."

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

"Hakan kuma bai yiwu ba kamar yadda nike tunani."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Akwai sauran aiki a gabanmu, da alamun akwai cin karo tsakanin matsayar gwamnati da kungiyar ASUU."
Adamu
Na Dade Ashe Yaudarar Kaina Cewa Zan Iya Magance Matsalar Yajin Aiki: Ministan Ilimi Hoto: Adamu
Asali: UGC

Daliban Najeriya Sun Roki Buhari Ya Yi Hakuri Ya Kawo Karshen Yajin ASUU

Kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta mika kokenta ga shugaban kasa manjo Muhammadu Buhari mai ritaya da ya yi hakuri ya kawo karshen yajin aikin malaman jami'a ASUU.

Daliban sun roki Buhari da ya daidaita da lakcarorin Najeriya domin ba su damar komawa makaratu su ci gaba da karatu.

Wannan batu na fitowa ne daga bakin shugaban NANS, Kwamared Usman Barambu a Abuja yayin zantawa da manema labarai.

Barambu ya koka da cewa yajin aikin ya kassara fannoni daban-daban na ilimin jami'o'in gwamnati tare da kawo kari ga shekarun kammala karatu ga dalibai.

Kara karanta wannan

Tura ta kaI bango: Daliban Najeriya sun gaji da yajin ASUU, sun tura wani sako ga Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel