Muhimman Abubuwa 7 da ya Dace a Sani Game Da Tukur Mamu, Hadimin Gumi da DSS Suka Kama

Muhimman Abubuwa 7 da ya Dace a Sani Game Da Tukur Mamu, Hadimin Gumi da DSS Suka Kama

  • Tukur Mamu Mazaunin Kaduna ne kuma mawallafin jaridar Desert Herald wanda ya jagoranci sasanci tsakanin 'yan ta'adda da iyalan fasinjojin jirgin kasa da aka sace
  • Malam Mamu yana da sarautar 'dan Iyan Fika a jihar Yobe kuma yana da matan aure hudu da 'ya'ya goma da suka hada da maza da mata
  • An sha kama shi a gwamnatin da ta gabata saboda wallafe-wallafe a jaridarsa da ka iya tada tarzoma kuma a kan kai samame ofishinsa dake Unguwar Sarki

Kaduna - Alhaji Tukur Mamu, wanda ya jagoranci sasanci tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin jirgin kasa da aka yi garkuwa da su a watan Maris, ya shiga hannun hukuma a birnin Cairo dake Misra a karkashin umarnin gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

Malam Tukur Mamu
Muhimman Abubuwa 7 da ya Dace a Sani Game Da Tukur Mamu, Hadimin Gumi da DSS Suka Kama. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Twitter

Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasa mai tsarki don yin Umra tare da iyalansa, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin sauka da tashin jiragen sama na Misra sannan aka dawo da shi Najeriya.

Ga wasu abubuwan da ya dace a sani game da mai sasancin da ‘yan bindiga, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

  1. Alhaji Tukur Mamu mazaunin Kaduna ne kuma mawallafin jaridar Desert Herald wanda ya assasa sasanci tsakanin ‘yan bindiga da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a farmakin jirgin kasa na 28 ga watan Maris din 2022.
  2. Yana da sarautar Dan Iyan Fika a jihar Yobe
  3. Alhaji Tukur Mamu yana auren mata hudu kuma yana da ‘ya’ya goma
  4. Hadimi ne a fannin yada labarai na Sheikh Ahmed Gumi, fitaccen malamin addini kuma tsohon soja mai mukamin kyaftin a NDA Kaduna.
  5. An sha kama Mamu a karkashin gwamnatin da ta gabata kan zarginsa da wallafe-wallafe da ka iya tada tarzoma.
  6. Kamfanin jaridarsa na nan a Unguwar Sarki kuma jami’an tsaro sun sha kai samame.
  7. Ya saba ayyuka mun al’umma da marasa karfi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta farin kaya ta tabbatar da kama Malam Tukur Mamu, tsohon mai sasanci tsakanin 'yan bindiga da 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Daily Trust ta rahoto yadda aka kama Mamu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar Laraba.

Mawallafin mazaunin Kaduna na fara kama shi a birnin Cairo dake Misra kuma an tsare shi na sa'o'i 24 kafin a dawo da shi gida Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel