Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

  • Tsagerun yan bindiga sun kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua a jihar Kaduna
  • Miyagun sun kuma kashe mutane biyu yayin da suka yi garkuwa da wasu da dama, sun kuma fasa shaguna
  • Harin ya biyo bayan samamen da dakarun rundunar sojojin Najeriya suka kai kan yan ta'adda a yankunan Birnin-Gwari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Jaridar Punch ta rahoto cewa yan ta’adda sun toshe hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

A yayin harin, maharan sun kashe akalla mutum biyu ciki harda wani direba yayin da suka sace mutane da dama.

Kaduna
Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama Hoto: Punch
Asali: UGC

Hakan ya kasance ne bayan GOC Division 1 na rundunar sojoji, Kaduna, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya jagoranci dakaru da suka kai samame kan yan ta’adda a yankunan Birnin Gwari rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa

Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Kasai, ya bayyana a ranar Litinin, cewa yan ta’addan sun koma hanyar Birnin-Gwari Funtua inda suka toshe yankin sannan suka kashe wani direba da sace matafiya da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, har yanzu matafiya basa iya bin hanyar. Ya ce rashin tsaro na kara tabarbarewa a hantar Birnin-Gwari zuwa Funtua da garuruwa da dama, musamman a yankin gabashin karamar hukumar.

Ya bayyana cewa yawancin garuruwan da ke wannan hanya irin su Kwasa-kwasa, Marabar Kwasa-kwasa, Nacibi, Farin Ruwa da sauransu sun zama wayam babu kowa saboda tsoron abun da ka iya zuwa ya dawo.

Ya kara da cewa:

“Yan fashi da makami sun sake kai farmaki garin Damari a ranar Talata 3 ga watan Satumban 2022 da misalin karfe 10:00pm inda suka kashe mutum daya tare da yashe shaguna. Hakan ya zo ne bayan mutanen da yan fashi suka fatattaka a watan Agusta sun fara dawowa garin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

“Yan bindigar sun kuma kai farmaki garin Layin Lasan a yammacin ranar Lahadi 4 ga watan Satumban 2022 inda aka sace mazauna da dama sannan aka tafi da su dazuzzukan da ke makwanta. Yan bindigar sun ci gaba da kai farmaki cikin sirri.”

Kasai ya bayyana cewa akwai bukatar a tura dakarun sojoji yankin kudancin Birnin-Gwari, musamman a yankunan Kakangi da Randagi wadanda ke raba iyaka da jihohin Zamfara da Neja.

Yayin da yake yaba kokarin gwamnati da dakarun sojoji, shugaban na BEPU, ya nemi a kai yaki zuwa mabuyar yan ta’adda a dazuzzuka don dawo da zaman lafiya ta yadda mutane za su koma garuruwansu ba tare da tsoro da razana ba.

Ya bayyana cewa akwai bukatar yin haka domin samar da damar yin zabukan 2023 a yankin ta yadda mutane za su aiwatar da yancinsu na zabe.

Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haream 200 Da Manyan Kwamandoji 5

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannun Yan Sanda Yayin da Suka Yi Yunkurin Sace Dan Takarar PDP

A wani labari na daban, mayakan Boko Haram sun sha kashi a hannun dakarun sojojin Operation Hadin Kai inda suka halaka mayakan kungiyar guda 200 ciki harda manyan kwamandojinsu guda biyar a jihar Borno, The Cable ta rahoto.

Dakarun sojojin sama da suka hada da bataliya ta 199 da ta 222 sun kaddamar da hare-haren ne a ranar 1 ga watan Satumban 2022.

Sojojin sun yi ruwan bama-bamai a mabuyar yan ta’addan a Gaizuwa wanda aka fi sani da Gabchari, Sheruri, Mantari da Mallum Masari, kauyukan karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel