Ku Cece Ni: DPO da Aka Yi Garkuwa da Shi, Ya Fadawa 'Yanuwa Wahalar da Yake Sha
- Ana neman watanni uku kenan da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da CSP Mohammed Gyadi-Gyadi
- Mohammed Gyadi-Gyadi DPO ne na rundunar ‘yan sandan Najeriya a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
- ‘Danuwan jami’in ‘dan sandan yace sun kai N5m, amma ‘yan bindiga suka tsare wanda ya kai masu kudin
Kaduna - A watan Yunin da ya gabata ne ‘yan bindiga suka dauke babban jami’in ‘dan sandan da ke kula da birnin Gwari a jihar Kaduna.
‘Yanuwan wannan jami’in tsaro sun shaidawa manema labarai cewa a halin yanzu Mohammed Gyadi-Gyadi yana cikin wani mawuyacin hali.
A ranar Talatar nan, Musa Muhammad Gyadi-Gyadi ya fadawa BBC Hausa, CSP Mohammed Gyadi-Gyadi yana tsare da sarka jikin kafafunsa.
Musa Gyadi-Gyadi yake cewa suna jin yadda miyagun ‘yan bindigan suke cin zarafin ‘danuwansa duk lokacin da suka tuntube su a wayar salula.
DPO yana kashin jini
“Muna magana ta wayar ‘yan bindigan. Jami’in ya fada mani cewa duk ruwan shekarar nan a kan shi ya sauka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kuma bai da lafiya, yana fama da borin jini. Ya roke mu da mu ceci rayuwarsa, ya fada mana sun sa masa sarka.
Yana ta rokonmu mu kubutar da su, domin yanzu yana fitar da bayan gidan jini, kuma kafafunsa suna ciwo."
- Musa Muhammad Gyadi-Gyadi
An karbe mai kai kudin fansa
Gyadi-Gyadi yake cewa wadanda suka dauke kaninsa sun bukaci a biya N250m da farko, daga baya suka rage kudin fansar zuwa 5m, wanda aka kai masu.
Da aka kai masu N5m, sai suka ce wannan duk na abinci ne. Daily Trust ta rahoto Malam Musa Gyadi-Gyadi yace yanzu an bukaci su karo kudi da babur.
Mun ji cewa da na-kusa da ‘dan sandan suka hada N2m, aka ba wani ya kai wa ‘yan bindigan, sai aka cafke shi, har yau ba a fito da wanda ya je kai kudin ba.
A taimaki rayuwar DPO - Abokin aiki
An ji wani abokin aikin wannan DPO yana mai kira na musamman ga gwamnati ta kubutar da CSP Gyadi Gyadi duk da hukuma ba ta biyan kudin fansa.
Abokin aikinsa yace watsi da shi a wajen ‘yan bindiga bai dace ba. Jami’in yace ‘yan sanda sun hada N5.6m da kyar, domin ‘yanuwansa ba su da wani hali.
Fasa gidan yari a Abuja
Kun samu rahoto Majalisar Tarayya na bincike a kan yadda ‘yan ta’adda suka fasa gidan yarin Kuje a watan Yuli, aka tsere da daruruwan mutane da dare.
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya je gaban kwamitin tsaro na majalisar kasar, amma yace ba zai yi cikakken bayani ba sai an kori manema labarai.
Asali: Legit.ng