Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ya Faru Ranar da Aka Fasa Gidan Kurkuku Kuje

Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ya Faru Ranar da Aka Fasa Gidan Kurkuku Kuje

  • Rauf Aregbesola ya je gaban kwamitin majalisar wakilai, ya bayyana abin da ya faru ranar da aka fasa gidan yarin Kuje
  • Ministan na harkokin gida na kasa ya shaidawa kwamitin tsaro akwai jami’an tsaro 65 da ke tsare da kurkukun a ranar
  • Da yake akwai ‘yan jarida a dakin taron kwamitin, Rauf Aregbesola bai iya zagewa ya yi bayanin abin da ya auku ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya yi karin haske a kan abin da ya faru lokacin da ‘yan ta’adda suka auka gidan gyaran halin Kuje.

Jaridar The Nation tace Rauf Aregbesola ya yi wannan bayani ne sa’ilin da ya bayyana a gaban wani kwamitin hadaka na majalisar wakilai a Abuja.

A cewar Ministan harkokin gidan, akwai jami’an tsaro 65 a lokacin da aka kai harin. Ana da sojoji, dakarun NSCDC sannan ga jami’an kula da shige da fice.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Ba Dakaru Wa’adi Domin Ganin Karshen ‘Yan ta’dda da ‘Yan Bindiga

Rauf Aregbesola yake cewa alhakin tsare gidan gyaran halin yana wuyan wadannan dakaru.

Jami’an tsaron da ke bakin aiki

“A wannan wuri a ranar da aka kai hari, akwai dakarun sojojin kasa 31, jami’ai biyar daga rundunar MOPOL, jami’an yaki da ta‘addanci 2 na ‘yan sanda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan sanda biyu daga rundunar ‘yan sanda na shiyyar Kuje, ma’aikata bakwai na jami’an kula da shige da fice na kasa, sai jami’ai uku daga NSCDC.
Akwai ma’aikatan ganduroba goma dauke da makamai." - Rauf Aregbesola
Kuje.
Bayan shiga gidan kurkukun Kuje Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Amma duk da yawansu, ba su iya hana ‘yan ta’adda su fasa gidan gyaran halin da ake ji da shi ba, kuma suka yi nasarar yin gaba da wasu mutane.

'Yan jarida sun hana a ji hakikanin magana

Premium Times tace shugaban kwamitin, Hon. Sharada Sha’ban ya nemi ayi zaman a kebe, amma abokan aikinsa irinsu Ifeanyi Momah ba su yarda ba.

Kara karanta wannan

APC ta Dakatar da Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Saboda Ya Hada-kai da PDP

Da yake akwai ‘yan jarida a wajen taron, Ministan ya ki yin cikakken bayani a game da adadin makaman da ke hannun wadannan jami’an tsaro a ranar.

Hon. Nicholas Ossai ya bukaci kwamitin ta gayyaci jami’an tsaro su zo domin suyi wa majalisar tarayya bayani, idan ba haka ba, a dauki mataki a kansu.

An dade ana neman jami'an tsaro su hallara a gaban kwamitin, amma sun ki zuwa.

Matsalar tsaro nan da Disamba

Kun ji labari shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a gama da duk wasu ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga ko kuma tsagerun da suka addabi kasar nan.

Legit.ng Hausa ta fahimci ba wannan ne karon farko da gwamnatin tarayya ta bada irin wannan wa’adi ba, an yi haka a 2015 wajen yaki da Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel