EFCC Ta Sake Kama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun Da Wasu Mutane 2 Kan Zargin Almundahana
- Hukumar EFCC ta sake kama kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo da wasu mutane biyu
- Olumo da wasu biyu za su fuskanci tuhume-tuhume 11 na karkatar da kudade da sauransu
- A halin da ake ciki, kakakin majalisar bai fitar da kowani jawabi dangane da lamarin ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta sake kama kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, kan zargin almundahana, jaridar Premium Times ta rahoto.
Mun dai ji cewa a ranar Alhamis da ya gabata, jami’an hukumar sun kama Mista Oluomo a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas.
Sai dai kuma, an saki kakakin majalisar a daren ranar Juma’a sannan aka nemi ya dawo ofishin hukumar a ranar Litinin.
A lokacin da kakakin majalisar ya koma ofishin na EFCC a ranar Litinin, sai aka tsare shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta ce Mista Oluomo da wasu mutane biyu da ake zargi suna tsare a hannun EFCC har zuwa karfe 9:43 na dare.
Rahoton ya kuma ce daga kakakin majalisar har hadiminsa, Abdulgafar Adeleye, basu amsa kiran waya ba balle a ji ta bakinsu kan lamarin.
Tuhume-tuhumen da ake yiwa Oluomo
Jaridar Punch ta rahoto cewa hukumar EFCC ta shigar da wasu tuhume-tuhume 11 a kan Mista Oluomo da magatakardar majalisar, Adedeji Adeyemo da akawun majalisar, Oludayo Samuel.
Har yanzu ba a kama cikon mutum da hudu da ake zargi ba, Adeyanju-Nimota Amoke, wanda ya kasance tsohon akawun majalisar.
Akwai yiwuwar za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu a ranar Talata.
Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa
A wani labari na daban, dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, ya karyata batun mallakar kadarori 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado.
Kyari ya ce sabanin rahoton cewa an gano makudan kudade a asusun bankinsa, naira miliyan 2.8 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wani N200,000 a asusunsa na Sterling, jaridar Leadership ta rahoto.
A cewar wata sanarwa daga lauyansa, Barista Hamza Dan Tani, duk zarge-zargen da NDLEA ke yi dangane da kudade da kadarori mallakar Abba Kyari karya ne.
Asali: Legit.ng