Majalisar Dattawa Ta Tona Wadanda da Suka fi ‘Yan Siyasa Sata da Rashin Gaskiya

Majalisar Dattawa Ta Tona Wadanda da Suka fi ‘Yan Siyasa Sata da Rashin Gaskiya

  • Shugaban kwamitin sauraron korafi a majalisa ya zargi ma’aikatan gwamnati da kwarewa wajen yin barna
  • Sanata Ayo Akinyelure (PDP, Ondo) yace ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa sata da kuma rashin gaskiya
  • Mafi yawan mutane sun fi damuwa da ‘yan siyasa, amma Sanatan jihar Ondo yace ba a nan kadai matsala take ba

FCT, Abuja - Kwamitin sauraron korafi na majalisar dattawa yace ya gano cewa ma’aikatan gwamnati sun fi kowa tafka rashin gaskiya a duk Najeriya.

Daily Trust ta rahoto shugaban kwamitin, Sanata Ayo Akinyelure yana cewa bincikensu ya nuna masu ma’aikatan sun fi ‘yan siyasa barna a kasar nan.

Ayo Akinyelure mai wakiltar yankin jihar Ondo a karkashin jam’iyyar PDP yayi wannan bayani ne a wajen wani taron karawa suna sani da aka shirya.

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

Mun fahimci an yi wannan taro na kwana biyu ne a garin Abuja domin fadakar da ma’aikatan gwamnati da na kamfanonin 'yan kasuwa a kan aikin ofis.

Inda matsalar ta ke - Sanata

Sanatan yake cewa kafin Muhammadu Buhari ya iya nasara wajen yaki da rashin gaskiya, dole ya kawo karshen barnar da ma’aikatan gwamnati suke yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto Ayo Akinyelure yana cewa abin da ya sa ma’aikatan gwamnati suke aikata ba daidai ba shi ne saboda sun fi ‘yan siyasa dadewa a bakin aikinsu.

Majalisar Dattawa
'Yan Majalisar Dattawa a zamansu Hoto: @NgrSenate
Asali: UGC

A dalilin shekarun da ma’aikata suke dauka a ofis, shiyasa ake fama da sata da rashin gaskiya.

‘Dan siyasar yake cewa ma’aikatan gwamnati sun kware a aikinsu domin sun yi shekaru 35, alhali ‘yan siyasa sai sun nemi tazarce bayan shekaru hudu.

A cewarsa, kafin a iya samun shugabanci nagari da gaskiya a wajen aiki, ya zama dole a rika bin doka a kamfanonin ‘yan kasuwa da ma’aikatun gwamnati.

Kara karanta wannan

Zan Siya Gida Kwanan nan A Birnin Lagas: In ji Mai Sana’ar Kifi, Mutane Sun Karfafa Mata Guiwa

Matsaloli sun yi yawa

A cikin matsalolin da al’umma ke fama da su yau, Akinyelure yace akwai rashin gaskiya, cin hanci, rashawa, sata, badakalar kwangiloli da raunin bankuna.

Baya ga wadannan matsaloli da suka shafi tattalin arziki, ‘dan majalisar yace Najeriya na yaki da rashin tsaro, wanda ya jawo ake rasa rayuka da dukiyoyi.

NNPC ta ba Tompolo kwangila

An samu rahoto cewa a kowane wata tsohon shugaban tsagerun MEND, Government Ekpemupolo watau Tompolo zai tashi da Naira Biliyan 4 daga hannun NNPC

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba tubabben tsageran kwangilar Naira biliyan 48. Wannan mataki da aka dauka ya raba kan wasu Gwamnonin jihohin Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel