Makaryaci Ne, Ba Shinkafa Yake Siyarwa Ba: Budurwa Ta Fallasa Matashi Mai Garkuwa Da Mutane

Makaryaci Ne, Ba Shinkafa Yake Siyarwa Ba: Budurwa Ta Fallasa Matashi Mai Garkuwa Da Mutane

  • Wata budurwa ta bayyana yadda wani abokinta da ke ikirarin yana sana’ar shinkafa ya shiga hannun yan sanda
  • Budurwar mai suna Ayyamuus a shafin Twitter ta ce kwatsam matashin ya yi mugun kudi sannan ya fara fantamawa
  • Ya siya motoci iri-iri da sabon gida har suka taya shi murna kawai sai suka gano cewa kazamar sana’a yake yi

Wata mai amfani da Twitter, Ayyamuus, ta bayyana yadda yan sanda suka kama wani abokinta kan zargin shiga harkar garkuwa da mutane.

A cewarta, matashin ya yi masu karyar cewa yana sana’ar siyar da shinkafa ne amma sai daga baya suka gano cewa duk karya ne.

Matashi da gida
Makaryaci Ne, Ba Shinkafa Yake Siyarwa Ba: Budurwa Ta Fallasa Matashi Mai Garkuwa Da Mutane Hoto: Abu Sanusi / Tom Sibley / Experience Interiors
Asali: Getty Images

Ya siya motoci da wani sabon gida kuma sun je har gidan don taya shi murnar bude gidan.

Sai dai kuma, yan watanni bayan nan, ta gano cewa ba sana’ar shinkafa yake yi ba, ana zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An Damke Matar Aure Kan Laifin Shirya Yadda Akayi Garkuwa Da Mijinta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yanzu matashin na nan tsare a hannun yan sanda kuma ba zai iya rayuwa a katafaren gidan da ya gina ba.

Ta ce:

“Abokin iyalinmu ya yi mugun kudi a farkon shekarar nan, ya siya sabon gida, motoci kuma mun taya shi murna, harma mun je ganin sabon gidan muka sa Albarka. Ya fada mana cewa yana sana’ar shinkafa. Kawai sai muka gano cewa shi din kasurgumin mai garkuwa da mutane ne. Yanzu haka, yana tsare a hannun yan sanda.”

Jama’a sun yi martani

Only Sogie ya rubuta:

“Na tabbata kin ci kin sha a bikin bude gidan. Na tabbata kin karbi kudi daga hannunsa. Me zai sa ki zo nan kina yi kamar tsarkakkakiya.

Joe Vancas ya ce:

“Shiyasa kada mu taba jinjinawa sauran masu kudi ba tare da sanin tushen kudinsu ba. Miyagu da dama suna ta bayar da sadaka a cocina.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

Abbas Lawal ya rubuta:

“Wannan abun bakin ciki da tausayi ne, a halin yanzu, ina shawartanki da kada aikinsa ya batar da ke zuwa ga tunanin haka a duk sanda kika ga wani ya yi nasara. Idan Allah yaso yana iya sa mutum ya zama mai kudi a dare daya.”

Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

A wani labarin kuma, wata budurwa da ba a gane ko wacece ba ta sha caccaka a wajen kawayenta a soshiyal midiya kan saka sunan saurayinta a da tayi a cikin kwalba.

A cewar yan matan a wani bidiyo da ya yadu, sun yi ikirarin cewa budurwar wacce ta kasance kawarsu ta daddaure kwalban kafin ta jefa shi a cikin rafi.

Yayin da suke kwancewa kawar tasu zani a kasuwa kan abun da ta aikata, sun koka cewa rayuwarsu suma tana cikin hatsari.

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Asali: Legit.ng

Online view pixel