An Damke Matar Aure Kan Laifin Shirya Yadda Akayi Garkuwa Da Mijinta

An Damke Matar Aure Kan Laifin Shirya Yadda Akayi Garkuwa Da Mijinta

  • Wata matar aure ta hada baki da yan bindiga don sace mijinta saboda mijin yana hanata saduwar aure sosai
  • Mijin ya bayyana cewa sai da ya biyasu kudin fansa naira milyan biyu don a sake shi
  • Garkuwa da mutane a Najeriya ya zama ruwan dare kuma mutane da dama sun rasa rayukansu

Uyo - Jami'an hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ranar Juma'a sun bayyana wata mata mai suna Joy Emmanuel wacce akewa zargin shirya yadda akayi garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.

Kwamishanan yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi, ya bayyanawa manema labarai cewa Joy tare da masu garkuwa da mutanen sun amshi N2million matsayin kudin fansa hannun mijin, rahoton PremiumTimes.

Me ya kaita haka?

Matar ta bayyanawa manema labarai cewa yanayi ya kai ta ga hada baki wajen garkuwa da mijinta.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi

Tace mijin bai saduwar aure da ita kuma ba ya kula da iyalinsa, riwayar DailyNigerian.

Tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kananan ayyuka nike yi don kula da iyalina. Na shirya garkuwa da shi ne don amfani da kudin wajen kula da iyalina."
"Abin takaicin shine ko da suka karbi kudin fansan ban samu ko sisi ciki ba."
"Sun karbi kudin amma basu bani ko sisi ba. Wadanda aka kama cikinsu ne suka fadawa yan sanda suna na."

Madam Joy tace Udo Moji shine shugaban masu garkuwa da mutanen da ta bawa aikin.

Police
An Damke Matar Aure Kan Laifin Shirya Yadda Akayi Garkuwa Da Mijinta
Asali: Twitter

Jawabin mijin matar

Mr Ebong yace anyi garkuwa da shine misalin karfe 8:30 na dare, ranar 21 ga Yuli.

Yace:

"Sun ajiyeni na tsawon kwanaki hudu kuma suka bukaci N2million."
"Sun ajiyeni a Etinan inda suka boye ni. Na ci sa'a yan sanda sun zo. Daga baya yan sanda sun kwace N500,000 daga hannunsu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel