Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamna Jang Daga Zargin Karkatar da N6.3bn

Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamna Jang Daga Zargin Karkatar da N6.3bn

  • A yau ne babbar kotun jihar Filato ta wanke tsohon gwamnan jihar. Jonah Jang bisa zarginsa da wawashe kudaden jihar
  • An shafe shekaru ana jiran ci gaba da sauraran shari'ar da aka fara ta tun 2018, an samu tsaiko a yayin shkari'ar
  • A kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafe wa gwamnoni biyu na Najeriya da suka wawashe kudin jiharsu

Jos, jihar Filato - Yanzu muke samun labari daga jaridar Punch cewa, a yau Juma'a 2 ga watan Satumba babbar kotu a jihar Filato ta sallami tsohon gwamnan jihar, Jinah Jang bayan wanke shi daga zargin rashawa.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Jang ne bisa zarginsa da laifukan karkatar da kudaden jiharsa da suka kai N6bn.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwani Adam Alkali Ya Yi Nasara A Kotu, An Fitittiki Dan Majalisar PDP Na Jos/Bassa

Kotu ta wanke tsohon gwamna daga zargin rashawa
Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamna Jang Daga Zargin Karkatar da N6.3bn | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A zaman nata na yau, kotun ta kuma sallami Yusuf Pam, wani tsohon mai karbar kudi na ofishin sakataren gwamnatin jihar Filato.

An gurfanar da Pam tare da tsohon gwamnan bisa zargi iri guda; zama kan wasu kudade na gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

EFCC ta gurfanar da Jang tare da Pam a watan Maris, 2018 a gaban mai shari’a Daniel Longji kan wasu tuhume-tuhume 17 na karkatar da N6.3bn mallakar gwamnatin jihar, rahoton Ripple Nigeria.

Mai shari’a Longji ya tafi a 2019, lamarin da ya kawo cikas ga ci gaba da sauraron karar na kusan sama da shekaru biyu.

Daga baya, an sake bankado karar 2020 lokacin da mai shari’a Christy Dabup, ya karbi aiki tare da karar.

Jonah Jang ya yi gwamna a jihar Filato tun shekarar 2007 zuwa shekarar 2015, shekarar da Buhari ya lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rushe ofishin kamfen na dan takarar gwamnan PDP saboda dalili daya

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

A wani labarin na daban, majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

Asali: Legit.ng

Online view pixel