Yan Ta'adda Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Hajiya Zainab Gummi Hari A Zamfara

Yan Ta'adda Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Hajiya Zainab Gummi Hari A Zamfara

  • Yan ta'adda sun kai wa ayarin motoccin kwamishinan mata da harkokin yara na Jihar Zamfara, Hajiya Zainab Lawal Gummi hari
  • Maharan sun bude wa ayarin motoccin kwamishinan wuta ne a ranar Talata a Kwanar Dogon Karfe kan babbar hanyar Sokoto zuwa Zamfara
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu ya ce sun fara bincike kan lamarin da nufin kama wadanda suka kai harin

Jihar Zamfara - Kwamishinan Mata da Harkokin Yara, Hajiya Zainab Lawal Gummi, ta tsallake rijiya da baya a yayin da yan ta'adda suka kaiwa ayarin motoccinta hari, rahoton HumAngle

Yan ta'addan sun bude wuta kan ayarin motoccin uku misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, 30 ga watan Agustan 2022, a Kwanar Dogon Karfe, kan hanyar Sakkwato - Zamfara a karamar hukumar Bakura.

Kwamishinan Zamfara
Yan Ta'adda Sun Kai Ayarin Motoccin Hajiya Zainab Gummi Hari A Zamfara. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

An tabbatar cewa kwamishinan, wacce ke kan hanyarta daga Sakkwato zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta tabbatar da harin amma ta ce lafiyarta kalau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Babu wanda ya samu rauni cikin mu saboda sauran kiris mu yi hatsari saboda wuta da yan bindigan suka bude mana."

An rahoto cewa yan ta'addan suna tsallake titin ne za su koma maboyarsu a lokacin da suka ci karo da ayarin motoccin kwamishinan, Sahara Reporters ta rahoto.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu ya ce ana bincike.

Ya kara da cewa:

"A halin yanzu rundunar tana bincike kan lamarin da nufin magance hare-hare a yankin da kuma gano wadanda suka kai harin domin hukunta su."

Idan za a iya tunawa a watan Yunin shekarar 2022, a hanyar na Sokoto zuwa Zamfara yan ta'adda sun sace mutane 50 da suka tafi halartar biki.

Gwamnan PDP Ya Ce Boko Haram Na Shirin Fara Kai Hare-Hare A Jiharsa

A bangare guda, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya bukaci sabon kwamandan 23 Armoured Brigade, Birgediya Janar Mohammed Gambo, ya taimakawa jihar magance matsalan tsaron cikin gida.

Birgediya Janar Gambo shine zai maye gurbin Janar A.M. Garba a matsayin kwamanda na 23 Armoured Brigade, bayan sauya-sauyen da babban hafsan sojojin kasa Lt. Janar Yahya Farouq ya yi.

Fintiri ya kuma bayyana cewa yan kungiyar ta'addanci na Boko Haram suna shirin sake kafa sansaninsu a jihar saboda kai hare-hare, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel