Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC A Abuja

Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC A Abuja

  • Rahotanni sun ce wasu matasa mambobin kungiyar daliban Najeriya, NANS, sun tafi sakatariyar APC da ke Abuja da nufin ganin Sanata Abdullahi Adamu
  • Wani ganau ya ce jami'an tsaro da ke tare da shugaban na APC sun nemi hana matasan shiga sakatariyar hakan kuma ya janyo rikici tsakaninsu
  • Rikicin ya yi kamari har ta kai ga jami'an tsaron sai da suka kira wadanda za su kawo musu dauki kafin suka iya tarwatsa fusatattun matasan da barkonon tsohuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Jami'an Tsaro da ke tsaron, Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC sun yi arangama da mambobin kungiyar daliban Najeriya, NANS, a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

Sakatariyar APC
Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Sakatariyar ta APC ta zama filin daga a yayin da yan sanda suka rika sakin barkonon tsohuwa domin su tarwatsa fusatattun mambobin na NANS, hakan yasa ma'aikatan sakatariyar suka rika neman wurin buya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

Nan take aka karo jami'an tsaro a kusa da sakatariyar sannan suka yi amfani da karfin suka tarwatsa fusatattun mambobin na NANs.

Shaidan gani da ido ya magantu

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce rikicin ya barke ne a lokacin da jami'an tsaron shugaban na APC, wai bisa umurninsa, suka yi kokarin hana mambobin na NANs shiga sakatariyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya daga hukumar tsaro ta yi bayanin cewa Segun Dada, mai neman takarar shugabancin kungiyar matasan Najeriya, wanda ya janye wa shugaban matasan na yanzu, ya jagoranci tawaga don yi wa shugaban jam'iyyar bayani kan zaben NANS.

Ta sake kacamewa a APC, Sanata Adamu ya dakatar da dukkanin daraktocin jam'iyya

A wani rahoton, kun ji cewa wata sabuwa ta sake kacamewa a gidan Buhari inda hankula suka tashi a sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa a ranar Juma'a sakamakon hukuncin shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu inda ya bukaci dukkan daraktocin jam'iyyar da su dakata da aiki har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

An Dakatar Da Wasu Yan Sanda Mata 2 Saboda Bidiyon 'Rashin Da'a' Da Suka Wallafa A TikTok

Bayan Adamu ya hau karagar shugabancin jam'iyyar a ranar 1 ga watan fairilu, ya bayyana cewa akwai yuwuwar ya sake gyara tsarin ssakateriyar jam'iyyar ta kasa.

A halin yanzu ya bazama gyara tsarin sakateriyar jam'iyyar inda ya mayar da ofishinsa kasa a maimakon hawa na uku da yake a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel