Gwamnan APC Ya Umurci Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Kamo Masa Sarki A Jiharsa

Gwamnan APC Ya Umurci Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Kamo Masa Sarki A Jiharsa

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bada umurnin a kama wani Mista Ademola Idowu Oloworiyibi da ke yin sojan gona a matsayin Olofun na Irele
  • Gwamnan ya ce gwamnatin jihar bata nada Mista Oloworiyibi sarauta ba kuma bata amince a nada shi sarauta ba don haka abin da ya ke aikatawa na iya tada zaune tsaye a jihar
  • Mista Idowu Oloworiyibi, baya ga yin sojan gona har ma yana nada wasu mutanen daban sarauta wadanda ba su san cewa ba shi bane halastaccen sarkin garin a cewar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Gwamnan Jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya umurci kwamishinan yan sanda, Oyediran Oyeyemi, ya kama Olofun na Irele, na karamar hukumar Irele, Oba Ademola Idowu a hukunta shi.

Gwamna Akeredolu ya ce Oloworiyibi sojan gona ne a gwamnatinsa kuma bai amince ba ko nada wani a matsayin Olofun na masarautar Irele, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Gwamnan PDP Ya Ce Boko Haram Na Shirin Fara Kai Hare-Hare A Jiharsa

Alleged Fake Monarch
Gwamnan Najeriya Ya Umurci Yan Sanda Su Kamo Masa Sarki A Jiharsa. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu mutane ne suka nada Oba Oloworiyibi a watan Yuli amma wasu sun yi korafi ga gwamnati suna cewa akwai abubuwan da hankalinsu bai kwanta da su ba.

Akeredolu ya bada umurnin a kama Oloworiyibi ne cikin wata wasika da ya tura wa CP na Ondo mai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan fadarsa, Cif Olugbenga Ale.

A wasikar da ya tura a daren ranar Laraba, Akeredolu ya bayyana ayyukan Oloworiyibi a matsayin haram da kuma wuce gona da iri.

Akeredolu ya ce hakan na iya kawo rikici tsakanin mutane masu son zaman lafiya a tsohon garin kuma abin da hakan zai haifar ba zai yi wa kowa dadi ba.

Wani sashi na wasikar:

"Gwamnati ta damu da abin da wani Mista Ademola Idowu Oloworiyibi, wanda ke gabatar da kansa a matsayin Olofon na masarautar Irele, karamar hukumar Irele na Jihar Ondo. Wannan sojan gonan har nadin sarauta ya ke yi ga wadanda ba su san ko shi wanene ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC A Abuja

"Matsayin gwamnatin jiha cewa bata nada wannan mutumin ko amincewa a nada shi a matsayin Olofun na masarautar Irele, don haka Mista Ademola Idowu Oloworiyibi mai laifi ne kuma abin da ya ke yi na iya janyo fitina a tsoron garin. Don wannan da wasu abubuwan, Gwamnatin Jihar Ondo na bada umurnin kama Mista Ademola Idowu Oloworiyibil tare da hukunta shi."

Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta nade hannu ta kyale wani ya tada zaune tsaye ba a jihar ya lalata zaman lafiyar da aka dade ana mora.

Sokoto: An Kama Dagajin Kauye Kan Dillancin Wiwi Da Miyagun Kwayoyi

A wani rahoton, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta ce ta kama dagajin kauyen Ruga, a karamar hukumar Shagari kan laifin sayar da muggan kwayoyi, Daily Trust ta rahoto.

Kakakin rundunar ta NDLEA ya ce an kama Alhaji Umaru Mohammed wanda aka fi sani da Danbala ne a ranar 22 ga watan Agustan 2022.

Kara karanta wannan

Barayin Mai: Gwamnati Ta Kawo Hujjar Ba Tsohon Tsageran N/Delta Kwangilar N48bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel