Ganduje Ya Soke Lasisin Filin da Bene Ya Kashe Mutane a Kano

Ganduje Ya Soke Lasisin Filin da Bene Ya Kashe Mutane a Kano

  • Gwamann jihar Kano ya soke filin da bene mai hawa uku ya danne mutane a Kano, ya ce ya yi karami da gina shaguna
  • Dakta Abdullagi Ganduje, wanda ya kai ziyara wurin ranar Laraba, ya ce ya kafa kwamitin fasaha da zai binciko musabbabin rushewar ginin
  • A ranar Talata, Ginin mai hawa uku ya rushe a Titin Beirut, kasuwar yan waya, mutum biyu suka rasa rayukansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙwace filin wurin da Bene mai hawa uku ya rushe a Beirut Road, kasuwar waya dake cikin birnin Kano.

Dailytrust ta ruwaito cewa Ginin wanda ya ruguje sanar Talata, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu yayin da wasu Bakwai ke kwance suna jinya.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje Ya Soke Lasisin Filin da Bene Ya Kashe Mutane a Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje/facebook
Asali: Facebook

Duk da cewa har yanzun ba'a tantance asalin masu wurin ba, amma shugaban hukumar ba da agajin gaggawa (SEMA), ya ce ginin ba'a yi shi yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

Lokacin da ya kai ziyarar domin ganin abinda ya auku ranar Laraba, gwamna Ganduje yace, "Tun asali kamata ya yi wurin ya kasance na aje ababen hawa, ya yi ƙanƙanta da yin Gini."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganduje ya ba da umarnin a maida wurin ya zama na aje ababen hawa, inda ya ƙara da cewa tuni gwamnatinsa ta kafa kwamitin fasaha mai ƙarfi da zai binciko musabbabin faruwar lamarin.

"Ya kamata mu sani cewa tun farko, duk wani wuri da za'a gina kamata ya yi kwararru su tsara shi kuma su sanya ido. Cikin mako ɗaya wannan kwamiti zai gama aikinsa ya kawo mana rahoto kuma zamu ɗauki matakin da ya dace."

'Yan kasuwa su bai wa mutane haɗin kai - Ganduje

Ganduje ya kuma roki 'yan kasuwa su baiwa ma'aikata haɗin kai yayin da suke kokarin tono tarkacen wurin domin kawar da su. Ya kara da cewa da zaran sun kammala gwamnati zata kawo kayayyakin maida filin wurin aje motoci.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

A wani labarin kuma An Ceto Mutum 3 Daga Ginin Da Ya Rufta A Kasuwar Kano, Akwai Saura Da Aka Kasa Fito Da Su

Wani gini mai bene biyu a kasuwar Kano ya rufta ya danne ma'aikata da yara masu talla da mai siyar da abinci a Beirut road da ke birnin Kano.

Jami'an tsaro masu bada dauki da suka kunshi yan sanda, jami'an kwana-kwana, ma'aikatan SEMA da jami'an FRSC sun isa wurin don taimako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel