Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah

Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah

  • Wata kabila yar asalin kasar Brazil ta shafe daga doron kasa bayan mutum daya da ya rage a cikinta ya kwanta dama
  • Mutumin ya rage shi kadai bayan kisan da aka yiwa sauran danginsa da suka rage a shekarar 1995
  • Ana yi masa lakabi da 'mutumin rami' saboda yawan ramukan da ya haka a yankin da yake inda a nan ne yake buya da kama dabbobi

Brazil - Hukumomi a Brazil sun sanar da labarin mutuwar wani mutum wanda shi daya tilo ne ya rage a cikin zuriyarsa yan asalin wata kabilar kasar.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa mutumin ya shafe tsawon shekaru 26 yana rayuwarsa cikin kadaici kuma ana yi masa lakabi da “Mutumin rami.”

Mutumin rami
Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah Hoto: brazzil.com
Asali: UGC

Wannan suna na mutumin rami ya samo asali ne sanadiyar ramuka masu zurfi sosai da ya haka kuma yake amfani da su wajen boyewa da kama dabbobi.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Rahoton ya nuna cewa an tsinci gawar mutumin ne a ranar 23 ga watan Agusta, a kusa da bukkarsa. Kuma babu wata alama da ke nuna an kashe shi ne saboda hargitsi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin shi daya ne ya yi saura a cikin mutane shida da suka rage a zuriya da kabilarsu, bayan kisan kiyashi da aka yiwa yan uwansu a shekarar 1995.

Yana dai zaune ne a yankin Tanaru da ke jihar Randomnia mai iyaka da Bolivia.

Mafi akasarin yan kabilarsa, an halaka su ne a farkon shekarun 1970, zamanin da masu kiwon dawakai suka amshe masu gonaki.

Hasashe sun nuna cewa marigayin zai kai kimanin shekaru 60 a duniya kuma ya kwanta dama ba tare da wata cuta ba.

Dan Shekaru 71 Ya Koma Makarantar Firamare, Bidiyo Ya Nuno Sa A Aji Tare Da Jikokinsa

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

A wani labari na daban, wani tsoho mai shekaru 71 wanda ya koma makaranta don samun ilimi ya burge mutane da dama a yanar gizo.

Tsohon mai suna Isaac ya kasance tsohon soja wanda bai kammala karatunsa ba kafin ya shiga rundunar sojojin.

Bayan ya yi ritaya, mutumin dan kasar Tanzaniya ya yanke shawarar komawa makaranta bayan ga cewa takwarorinsa sun yi masa nisa a bangaren ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel