'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Filato

  • 'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida da daddare sun halaka tsohon Sakataren PDP a gundumar Mangu dake jihar Filato
  • Bayanai sun nuna cewa mutane sun tsinci gawar wani mutumi a gefen Titi kusa da ƙauyen Dangoer, inda aka kashe jigon PDP
  • Mazauna yankin sun nemi gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin kauce wa faruwar haka nan gaba

Plateau - 'Yan bindiga sun kashe tsohon Sakataren tsare-tsare na Jam'iyyar PDP a gundumar Mangu 1, ƙaramar hukumar Mangu, a jihar Filato, Nehemiah Goholshak.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Goholshak ya rasa rayuwarsa ne yayin da 'yan bindigan suka kutsa cikin gidansa a yankin.

Wani mazaunin yankin, Chris Yakubu, wanda ya zanta da 'yan jarida a Jos ranar Litinin, ya ce lamarin ya auku ne ranar Asabar da daddare.

Kara karanta wannan

2023: An Sanya Lokacin Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP, Atiku Zai Fara Zawarcin Wasu Yan Siyasan Kano

Taswirar jihar Filato.
'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP a Jihar Filato Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yakubu ya bayyana cewa mutane sun tsinci wata gawa da ba'a san ko waye ba a wannan rana a gefen titin Mangu-Bokkos kusa da yankin da aka kashe tsohon Sakataren PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda maharan suka kashe tsohon Sakataren PDP

A kalamansa yace, "Yanzun muka dawo daga kai ziyarar jaje ga iyalan gidan su Nehemiah Goholshak, ɗan shekara 30, wanda 'yan bindiga suka harbe har lahira ranar 27 ga watan Agusta, 2022."

"Marigayin tsohon Sakataren tsare-tsare ne na jam'iyyar PDP a gundumar Mangu 1, karamar hukumar Mangu. Yana zaune a gidansa dake ƙauyen Dangper lokacin da maharan suka shigo suka kashe shi wajen karfe 7:00 na dare."

"Kawunsa Mr Timothy Goholshak, ya tabbatar da mutuwarsa nan take, saboda haka aka yi jana'izarsa jiya (Lahadi) kuma tun wannan lokacin mutanen ƙauyen suka shiga cikin jimami. Ban ji daɗi ba saboda haka ta faru da yayansa a gidan."

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Mista Yakubu ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara tsaurara bincike a yankim domin daƙile faruwar irin haka nan gaba, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, bai ɗaga kiran wayar salula da aka masa domin yin tsokaci kan lamarin ba.

A wani labarin kuma Wasu 'Yan Bindiga Sun Datse Hannuwa Biyu Na Wani Mutumi a Jihar Zamfara

Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sare hannuwan wani mutumi a jihar Zamfara.

Ɗan uwan mutumin ya labarta yadda maharan suka shigo ta tsiya cikin gida suka aikata wannan ta'asa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel