Yajin aiki: Wasu Jami’o’i Na Ta Botsarewa ASUU, Za Su Koma Bakin Aikinsu Yau

Yajin aiki: Wasu Jami’o’i Na Ta Botsarewa ASUU, Za Su Koma Bakin Aikinsu Yau

  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai daina biyan malaman jami’ar jihar Gombe muddin dai ba su koma aiki ba
  • Mai girma Gwamnan yace tun da kungiyar ASUU ta tafi yajin-aiki ake biyan malamai, ba tare da sun yi aikinsu ba
  • Shugaban jami’ar jihar Ekiti ya bada sanarwar cewa yau za su cigaba da karatu duk da ba sasanta da ASUU ba tukuna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi gargadin gwamnatinsa za tayi koyi da gwamnatin tarayya a kan yajin aikin ASUU.

A ranar Litinin, 29 ga watan Agusta 2022, aka rahoto Muhammadu Inuwa Yahaya yace zai dakatar da albashin malaman jami’arsa idan suka ki dawowa aiki.

Mai girma gwamnan ya yi wannan bayani ne a shirin ‘A Fada A Cika’ da ake yi a BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar Zartaswar ASUU Zata Shiga Ganawa, Za’a Yanke Shawara Kan Lamarin Yajin Aiki

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yake cewa duk tsawon watanni shida malaman jami’ar jihar Gombe ta GSU suke yajin-aiki, ana biyansu kudi.

An gagara shawo kan ASUU a GSU

A cewarsa, an yi kokarin tattaunawa da shugabannin jami’ar ta GSU da kuma reshen kungiyar ASUU na malaman jami’ar GSU, amma an gaza samun mafita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan har malaman sun ki bude jami’ar domin a cigaba da karantar da yara kamar yadda aka bada umarni, gwamnatin jihar Gombe za ta daina biyan albashi.

Jami'ar GSU
Jami'ar Jihar Gombe Hoto: gsu.edu.ng
Asali: UGC

An rahoto Gwamnan yana bayanin yadda yake biyan ma’aikatan jihar da ‘yan fansho albashinsu duk ranar 25 da 27 na kowane wata tun da ya zama gwamna.

Kwanaki aka ji labari daga Daily Trust cewa a ranar Litinin da ta wuce za a dawo aiki a jami’ar. ASUU tace za tayi bayani a game da batun a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

An Yanke Wutan Gidan Gwamnati da Ofisoshi Saboda Rashin Biyan Kudin Lantarki

EKSU za ta bude aji inji VC

Bayan haka kuma, This Day ta kawo labari cewa shugabannin jami’ar EKSU da ke Ado Ekiti a jihar Ekiti za su koma aiki, ko da ba a sasanta da ASUU ba.

Shugaban jami’ar jihar, Farfesa Edward Olanipekun ya bada sanarwar za su ballewa kungiyar ASUU, su cigaba da koyar da daliban na su daga makon nan.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani a ranar Lahadi, Edward Olanipekun yace sun dauki wannan mataki ne bayan ganin cewa an dauki lokacin ana yajin-aiki.

EKSU ta nuna fushinta kan yadda shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya soki jami’o’in jihohi, ta kai EKSU ta bukaci ya nemi afuwa.

El-Rufai v ASUU

Kwanaki muka rahoto cewa Mai girma Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yace Malaman jami’ar jihar Kaduna ba su da dalilin biyewa kungiyar ASUU.

El-Rufai ya sha alwashin dakatar da albashin marasa zuwa aji, zai maye gurbinsu. Bayan nan aka samu labari an dawo aiki, har an yi jarrabawa a KASU.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar Malaman Jami’o’i Su Shiga Yajin-Aikin Da Babu Ranar Dawowa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng