Gwamnonin da suka gudu Abuja saboda rikicin makiyaya matsorata ne - Minista

Gwamnonin da suka gudu Abuja saboda rikicin makiyaya matsorata ne - Minista

- Ministan Wasanni da Cigaban Matasa, Solomon Dalung, ya koka da Gwamnonin da su ke korafi kan rikincin makiyaya a Jihohin su

- Ya ce abun kunya ne da ragonci gazawar su na shawo kan lamarin da kuma kai koken su zuwa Abuja

- Ya kuma karyata rade-radin cewar zai fito takaran Gwamnan Jihar sa ta Filato

Ministan Wasanni da Cigaban Matasa, Barista Solomon Dalung, ya bayyana kai kukan da Gwamnan Benue da wasu Gwamnonin su ka yi na rikicin makiyaya a Jihohin su a mastayin abun kunya da ragonci.

Ya bayyana hakan ne yayin karyata rade-radin cewa zai fito takaran Gwamnan Jihar sa ta Pilato. Dalung ya ce abun kunya ne yadda Gwamna mai cikakkiyar iko zai tsaya ya na kuka kan lamarin da ya ke da ikon magancewa.

Gwamnonin da suka gudu Abuja saboda rikicin makiyaya matsorata ne - Minista
Gwamnonin da suka gudu Abuja saboda rikicin makiyaya matsorata ne - Minista

KU KARANTA: Zargin Rashawa: Za a gurfanar da Ciyaman din CCT ranar 16 ga watan Maris

Ya kuma ce hakkin kula da rayuka da dukiyar al'ummar Jiha ya rataya ne kan wuyan Gwamnoni. Abun kunya ne kuwa gare su gaza sauke wannan nauyi. Ya kuma yabawa al'ummar Jihohin bisa jajircewar su da nuna rashin tsoro na tabbatuwa a wuraren zaman su.

A game da fitowar sa takaran Gwamnan kuwa, Dalung ya ce bai san inda a ka samo wannan karya ba. A cewar sa, a yanzun dai ba shi da burin fitowa takaran ko da kansila ne ballantana Gwamnan.

Ya ce nauyi da dawainiya da ke kan Gwamna su na da yawan gaske. A cewar sa, shi ba zai nemi ya daurawa kan sa hawan jini ba sakamakon wahalan kasancewa Gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164