Mai Dakin Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ta Na Neman Alfarma Wajen Gwamnatoci

Mai Dakin Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ta Na Neman Alfarma Wajen Gwamnatoci

  • Matar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta roki gwamnatoci su taimakawa masu fama da cutar sukari
  • Bola Obasanjo ta halarci wani taro da matasa suka shiryawa wadanda suke dauke da ciwon suga daga yankunan kasar nan
  • Mai dakin ta Cif Olusegun Obasanjo tayi kira ga masu larura su rika kiyaye dokoki da kuma sharudan malaman asibiti

Ogun - Matar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, Bola Obasanjo tayi kira ga gwamnatoci a kowane mataki su kula da masu ciwon sukari.

Punch ta rahoto Misis Bola Obasanjo tana cewa ya kamata gwamnatoci su rika daukar dawainiyar marasa hali da suke fama da ciwon sukari.

Matar tsohon shugaban tace kudin da ake kashewa wajen maganin ciwon sukari yana da matukar yawa, don haka marasa lafiya ke neman taimako.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Obasanjo tace akwai bukatar masu kudi da gwamnatoci su rika agazawa masu fama da larurar.

Jaridar tace dattijuwar tayi wannan bayani ne a wajen wani taron kwana biyu da matasan jigar Ogun suka shirya a cibiyar Talabi Diabetes Centre.

Kamar yadda muka samu labari, taron ya samu halarcin mutane 29 daga kowane yanki na kasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Obasanjo
Mai Dakin Tsohon Shugaban Kasa Hoto: Punch
Asali: UGC

Kira ga mutanen jihar Jigawa

Mai dakin Obasanjo ta fadawa masu fama da ciwon da suka zo daga jihar Jigawa ya kamata kwamishinoni da gwamnati ta taimaka masu da magani.

Bola Obasanjo take cewa cutar sukari na da tsadar kula, kuma za a iya cewa bai da tsada sosai. Abin da kawai za a iya shi ne a nemi taimakon hukuma.

“Idan ba ku fada masa ba, su (gwamnatoci) ba za su sani ba. Akwai abubuwa da yawa a gabansu. Sai kun sanar da su tukuna, sai su taimaka maku.”

Kara karanta wannan

Hamisu Wadume: An sake Sojojin Da Suka Kashe Yan Sanda, Har An Karawa Kyaftin Balarabe Girma

- Bola Obasanjo

A bi shawarar Likitoci - Bola Obasanjo

Baya ga neman taimako, Bola Obasanjo ta bada shawara ga mahalarta taron da suyi amfani da shawarwarin da masu rayuwa lafiya kalau da cutar suke ba su.

Mai gidanta Obasanjo yana cikin wadanda sun dade su na fama da ciwon sukari, amma har yau yana rayuwarsa saboda ya kiyaye abin da Likitoci suke fada.

Gwamna zai koma mawaki

A baya kun ji labari Gwamna Oluwarotimi Akeredolu yace abin da yake hari da zarar ya bar kan kujerar Gwamnan Ondo shi ne ya zama fitaccen mawakin coci.

Oluwarotimi Akeredolu wanda kwararren Lauya ne yake cewa zai koyi amfani da fiyano domin ya rika rera wakokin bege a matsayinsa na mai kunar Yesu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel