Sojojin Najeriya Za Su Shiga Yajin Aiki, Malamin Addini Ya Hango Matsaloli Ga Najeriya

Sojojin Najeriya Za Su Shiga Yajin Aiki, Malamin Addini Ya Hango Matsaloli Ga Najeriya

  • Har ila yau, fitaccen malamin addini kirista, Primate Elijah Ayodele ya sake hango wasu matsaloli ga Najeriya a kwanan nan
  • Malamin ya ce, 'yan Najeriya za su shiga wani mummunan yanayi, kuma sojojin kasar za su tsunduma yajin aiki saboda tabarbarewar tattalin arziki da kuma bashin da ake bin kasar
  • Ba wannan ne karo na farko da wannan malamin addini ke hango wasu abubuwa ga Najeriya ba, sai dai, shin suna faruwa da gaske?

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya ce 'yan Najeriya su shirya dandana kudarsu a wani yanayi mafi wahala da zai faru sakamakon matsin da gwamnati sanya kasar.

Ya bayyana cewa, wannan hasashe nasa zai faru ne cikin shekaru shida kacal da ke tafe, inda abubuwa marasa dadi za su faru a Najeriya.

Hasashen wani fasto game da makomai Najeriya bayan mulkin Buhari
Sojojin Najeriay za su shiga yajin aiki, malamin addini ya hango matsala ga Najeriya
Asali: UGC

Faston dai ya yi wannan sharhi ne a ranar Jumma'a, 26 ga watan Agusta a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Osho Oluwatosin ya fitar, PM News.

Kara karanta wannan

N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki

A hasashen nasa na gargadi, faston ya bayyana cewa, mutane sun kusa fara zanga-zanga game da tabarbarewar tattalin arziki saboda abubuwa za su yi tsada mafi muni a 'yan kwanaki masu zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani rahoto na Daily Post kuwa, malamin ya ce, nan kusa za a fara siyar da man fetur N250 kan kowane lita, buhun siminta N6,000 ruwan leda kuwa N50.

Rundunonin tsaro za su tsunduma yajin aiki - hasashen Primate Ayodele

Faston bai tsaya nan ba, ya ce halin da kasar nan ke ciki ya kai intaha, domin kuwa ‘yan sanda da sojoji za su shiga yajin aiki bisa ganin gazawar gwamnati wajen biyansu albashi.

Ya kuma hango cewa, ababen tafiyar da rayuwa, musamman kayan abinci, za su yi tashin gwauron zabi, kuma zai yi wahala ‘yan kasar su iya da kansu.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Kano Sanusi ya ba 'yan Najeriya shawarin shugaban da za su zaba

Mafita

Sai dai, malamin bai tsaya iya batun matsaloli da babatun bayanai ba, ya bayyana kadan daga mafitan da gwamnati ya kamata ta duba.

A cewarsa, idan har gwamnati na son magance matsalolin, dole ne ta karfafa kayayyakin da ake kerawa a gida Najeriya sannan ta tallafawa masu sana’ar kere-kere.

Hakazalika, ya ce kada gwamnati ta manya da inganta noma, ta samar da ayyukan yi ga matasa, kana ta yi garanbawul ga abubuwa da dama na tsarin gwamnati.

Primate Ayodele ya bayyana abun da zai samu APC da PDP gabannin 2023

A wani labarin, babban limamin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya saki sabon hasashe game da babban taron jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da rikicin people democratic party (PDP).

A wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin labaransa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya bayyana cewa babban taron APC zai yi sanadiyar rugujewar jam’iyyar mai mulki idan ba su daidaita abubuwa ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnonin Najeriya sun ba lallai a yi zabe a wasu jiohohin Arewa ba a 2023

Ya bayyana cewa korarren shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni ba zai ga rahamar wasu gwamnoni ba, sannan cewa yunkurin gwamnoni na saisaita abubuwa zai kara haddasa rikici cikin jam’iyyar, PM News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.