An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso

An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso

  • Bayan diramar da ya faru a jihar Borno ranar Alhamis, an bude sakatariyar jam'iyyar NNPP ta jihar
  • Jam'iyyar ta NNPP ta zargi gwamnan jihar Babagana Zulum da alhakin kulle ofishin da kama shugabanta
  • Shugaban APC na Borno, Ali Bukar Dalori ya musanta cewa jam'iyyarsu na da hannu kan lamarin, ya shawarci NNPP ta warware matsalarta da yan sandan

Maiduguri - An bude ofishin jam'iyyar New Nigeria People Party NNPP na jihar Borno kwana daya bayan garkameshi da aka yi ranar Laraba.

Saifullahi Hassan, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa karkashin jam'yyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Hassan yace bayan haka gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada hakuri bisa abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bene Mai Hawa Biyu ya Ruguje, Ya Danne Ma'aikata Masu Tarin yawa a Abuja

A cewarsa

"An bude Sakatariyar jam'iyyar @OfficialNNPPng da aka rufe jihar tare da bamu hakuri daga Gwamna."
"Mun godewa yan Najeriya da suka tayamu caccakar wannan abin takaici da aka yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

JamiyyarNNPP
An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso
Asali: UGC

Yan Sanda Sun Rufe Sabuwar Ofishin NNPP A Borno, An Kuma Kama Shugaban Jam'iyyar

Jami'an tsaro dauke da bindigu da aka zargin yan sanda ne, a safiyar ranar Alhamis sun mamaye sakatariyar jam'iyyar NNPP da ke Maiduguri, Jihar Borno kwanaki kadan kafin kaddamar da ofishin da ke kusa da Abbaganaram.

Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne a ranar Laraba bayan da shugabannin jam'iyyar suka dauki hayar leburori su musu fentin sabuwar sakatariyar, gabanin zuwan dan takarar shugaban kasarsu, Rabiu Kwankwaso don kaddamar da ofishin.

Amma, wasu da ake zargin yan daba ne daga jam'iyyun hamayya suka kutsa sakateriyar suka lika fastocin yan takarar su a wurare daban-daban a harabar sakateriyar.

Kara karanta wannan

Rikici: Basarake ya mance da batun rawani ya tsere yayin da 'yan daba suka farmaki fadarsa

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

Kwankwaso a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.

Amma, duk da hakan ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyarsu ta NNPP su kwantar da hankulansu tare da kasancewa masu bin doka da oda a yayin da suke kokarin warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel