Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Je Har Wajen Shagalin Biki Suka Kama Amarya Kan Zargin Sata
- Rundunar yan sandan Uganda tana tuhumar jami’anta hudu a kan mamaye wani liyafar aure tare da kama amarya
- Jami’an yan sandan sun kai samame wajen shagalin biki sannan suka cafke amaryar kan zargin yin sata
- Lamarin ya jefa angon da mahalarta taron cikin rudani yayin da kowa ya yi zuruzuru don amaryar ta kwana ne a kurkuku
Uganda - An tashi zuru-zuru a wajen wani liyafar aure bayan jami’an yan sanda sun farmaki wajen taron sannan suka kama amaryar a kan zargin sata.
Shafin LIB ya rahoto cewa na tsaka da gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a makarantar Kimiyya ta Kakiika da ke birnin Mbarara, Uganda, lokacin da jami’an tsaron suka zo suka tafi da amaryar Ms. Christine Natuhera sannan suka garkame ta.
An kama ta ne kan zargin cewa ta saci kudi daga tsohon wajen aikinta.
Manajan wajen da ta yiwa aiki mai suna Mirembe Henry, ya zarge ta da yiwa kamfanin sata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da ake binciken lamarin a matsayin tuhumar aikata laifi, yan sanda sun shawarci bangarorin biyu da su nemi mafita a karshen Yuli, a cewar wata sanarwa ta rundunar yan sanda.
Daga nan sai aka kori shari’ar saboda rashin hujja.
Sai dai kuma, bayan sake bude shari’ar a watan Agusta, shugaban yankin ya yanke shawarar tuhumar matar da sata sannan ya yi umurnin kama ta.
Rundunar yan sandan ta ce jami’an da ke da hannu a lamarin sun haddasa fargaba a cikin mutane sannan cewa sun aikata hakan ne bisa umurnin tsohon shugabanta Henry.
Rahoton ya bayyana cewa da motar Henry suka yi amfani wajen daukarta zuwa kurkuku.
Angon, Mista Edson Tumukunde, ya ce shi da sauran baki da suka hallara wajen liyafar sun yi kokarin ganin ba a kama amaryar tasa ba.
Mista Tumukunde ya ce:
“Bakin da ke wajen sun yi yunkurin dakatar da su. Wata mata ta cafke gashin matata sannan ya fitar da ita daga tsari.”
Daya daga cikin yan bikin ta cafke Ms Natuhera daga hannun jami’an sannan ta tura ta cikin mota don tserewa da ita, amma sai yan sandan suka gaggauta bin sahunsu.
Daga bisani jami’an yan sandan suka kama su sannan suka tafi da amaryar zuwa ofishinsu.
“Ta kwana ne a kurkuku. Bakinmu sun tsaya a wajen liyafar har zuwa karfe 1:00 na tsakar daren Asabar yayin da muke ta kokarin ganin an saketa,” in ji angon nata.
A yanzu rundunar yan sandar ta bayar da hakuri a cikin wani jawabi da ta saki.
Kwamandan yan sandan yankin Rwizi, Mista Ezekiel Emitu Ebapu, ya zargi jami’an da haddasa rikicin son zuciya sannan ya bayar da hakuri kan yadda aka tafiyar da lamarin amaryar.
Mista Emitu ya ce:
“Wannan al’amarin abun takaici ne ainun. Da kamata yayi ace su jira ta kammala abun da take yi sannan su kama ta.”
Jawabin ya kara da cewa:
“Kamun nata cin mutunci ne a gaban ango, yan uwa, abokai, baki da surukanta.
“Ya zama cewa abun da ya kamata ya zama ranar farin ciki a rayuwarta ya zama mafarki mai ban tsoro.”
A karin bayani da rundunar ta sake saki, ta bayyana cewa jami’an da suka yi kamun suna nan a gidan maza yayin da wasu uku suka tsere, BBC Pidgin ta rahoto.
An kama Sajan Richard Ngabirano, wani jami'in bincike, yayin da wasu kananan yara uku da suka hada da Caroline Adio, Atugonza Muganyizi da Moris Ayesiga suka gudu.
Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga
A wani labarin, wani matashi dan Najeriya mai suna Abdul Afeez Jubril ya nuna farin cikinsa sakamakon wani karamci da mutanen Najeriya suka nuna masa.
A cewar Alfulanny Sebilu Nnajat a Facebook, an yankewa Abdul zaman shekaru 12 a gidan yari bisa kuskure a wani shari’ar fashi da makami.
Yayin da yake gidan yari, Abdul Afeez ya koyi yadda ake wanki da guga, kuma wannan horo ya taimaka masa bayan ya fito daga kurkuku.
Asali: Legit.ng