‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Yana Neman Kashe Tsohon Shugaban Majalisa
- Kwanan nan tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa ya rubuta takarda zuwa ga IGP, yana cewa akwai masu neman hallaka shi
- Ana haka sai ga labari ‘Yan sanda sun yi ram da wani mutumi, wanda da bakinsa ya amsa cewa yana neman yadda zai kashe Hon. Yakubu Dogara
- Mutumin ya dauko wata hadisa da ta faru a Tafawa-Balewa tsakaninsa da ‘Dan siyasar a 2021, a dalilin haka yake neman yin wannan aika-aika
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bauchi - Daya daga cikin wadanda ake zargi da yunkurin ganin bayan Yakubu Dogara, sun shiga hannun ‘yan sanda kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Bauchi sun cafke wani wanda ake zargin yana cikin masu kokarin kashe tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya.
Kwamishinan ‘yan sanda na Bauchi, Umar Mamman, ya shaida cewa wannan mutum da aka kama, ya nuna akwai jikakka tsakaninsa Yakubu Dogara.
CP Umar Mamman yake cewa sun samu labari a game da zargin, sai suka soma yin bincike.
“Mun samu labari cewa wasu jami’anmu na kokarin saida bindiga, sai muka bincike su, kafin nan mun ji labari yana yawo da bindigogi a motarsa.
Da muka same shi, sai muka tambaye shi a game da motar, da muka laluba sai ga bindigogi.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- CP Umar Mamman
Kamar yadda Leadership ta fada, da bincike ya yi nisa, ‘dan sandan ya tona asirin wanda ya ba shi bindiga, ya kuma ce yana shirin saida makaman ne.
“Da muka cigaba da bincike, sai ya fada mana wani a garin Tafawa Balewa ne ya same shi, yana neman bindigar saidawa, shiyasa yake yawo da ita.
Da ya bamu sunansa, sai muka cafke shi. Shi kuma ya fada mana yana neman bindiga ne saboda wani mummunan abin da ya faru a Disamban 2021.
- CP Umar Mamman
Daily Trust tace wannan mutum ya ambaci sunayen wasu mutane, daga ciki har da tsohon shugaban majalisa, yace yana nemansa domin ya ga bayan shi.
Mamman yake cewa sun yi amfani da hikima wajen tatsar bayani daga ta’aliki, ya kuma tabbatar da cewa ana yin bincike a kan bindigogin da suka bace.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an ji Rt. Hon. Dogara ya rubuta takarda zuwa ga shugaban ‘yan sanda na Najeriya yace rayuwarsa ta na cikin barazana.
Bola Tinubu ya yi kuskure - Dogara
Kwanaki an ji labari Yakubu Dogaraya yi kaca-kaca da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC a 2023 saboda ganin an dauki Musulmai biyu.
A kan wannan ne wasu Kiristocin Arewa suka gudanar da babban taron a birnin tarayya Abuja. Dogara da ya samu halarta, yace Tinubu ya yi kuskure.
Asali: Legit.ng