Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi

Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi

  • Tsohon jakadan Najeriya a kasar Philippine, Yemi Farounbi, yace Ubangiji na amfani da Buhari ne wurin ladabtar da 'Yan Najeriya
  • Farounbi yace an ankarar da 'yan Najeriya kan tarihin shugaba Buhari amma suka yi kunnen uwar shegu, suka zabe shi
  • Ya kara da jaddada cewa, wadanda ke shakatawa daga cin hanci, rashawa, rashin tsaro, nakasassar wutar lantarki, suke jin dadin kasar

Yemi Farounbi, tsohon ambasadan Najeriya a kasar Philippine, yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ladabtarwar ce daga Ubangiji da ake yi wa 'yan Najeriya.

The Cable ta ruwaito cewa, Farounbi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da aka tattauna da shi a shirin gidan rediyo a Ayekooto a Splash 105.5FM.

Yace an ja kunnen 'yan Najeriya kan tarihin Buhari da kuma yadda ya garkame 'yan siyasa massu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Yemi Forounbi
Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi. Hoto daga thecableng
Asali: UGC
"A 2014 zuwa 2015 lokacin da 'yan Najeriya suka yanke shawarar karbar kamfen din, an ja musu kunne kan tarihin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yadda ya garkame 'yan siyasa da suka hada Chif Obafemi Awolowo," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ubangiji yana da abun mamaki. Ya yanke shawarar yin amfani da Buhari wurin ladabtar da shaidancin 'yan Najeriya, kuma 'yan Najeriya sun cancanci ladatarwa.
“Najeriya ba yadda nake tsammani take ba. Ina da tabbacin Najeriya zata cigaba. Wadanda ke mora daga kudin cin hanci, rashawa, nakasassar wutar lantarki, rashin tsaro da sauransu basu fatan Najeriya ta cigaba."

Tsohon ambasadan ya kara da cewa barazanar da 'yan bindiga suka yi ga Buhari da Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana babbar matsala ga hadin kan kasar nan.

Shugaba Buhari Ya Maida Tsohon Hadiminsa, Bashir Ahmad, Ya Ba Shi Babban Matsayi

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Sake Naɗa Tsohon Hadiminsa da Ya Yi Murabus, Ya Ba Shi Babban Matsayi

A wani labari na daban, Shugaban kasa, Muhammadu Buhati, ya naɗa tsohon mai taimaka masa kan harkokin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, a matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan sadarwar zamani.

Hukumar Dillancin labarai ta kasa (NAN) ta rahoto cewa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya tabbatar da naɗin da wata takardar ɗaukar aiki da ya aike wa Bashir Ahmad, ranar 20 ga watan Yuli.

A takardar wacce NAN ta ci karo da ita ranar Lahadi a Abuja, Mustapha ya ce naɗin ya fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel