Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Biliyoyin da Ake ci Duk rana a Tallafin Man Fetur

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Biliyoyin da Ake ci Duk rana a Tallafin Man Fetur

  • Kwamiti na musamman da zai yi bincike a kan lamarin tallafin man fetur a Majalisar wakilan tarayya ya soma yin zama
  • An kira Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki domin tayi wa kwamitin karin haske a kan abin da ake kashewa
  • Zainab Ahmed ta fadawa ‘Yan majalisar tarayyar cewa gwamnati na yi wa ‘yan kasa rangwamen fiye da N200 a duk litan mai

Abuja - Mun samu labari kwamitin da aka kafa a Majalisar wakilan tarayya domin bincike a kan tallafin man fetur ya fara aiki a birnin tarayya Abuja.

Gidan rediyon FRCN yace kwamitin na musamman ya fara yin zama da Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed a majalisa.

Da aka gayyaci Ministar a gaban kwamitin domin tayi karin haske, ta shaida cewa gwamnatin tarayya na biyan N283 a matsayin tallafi a duk litar mai.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

Abin da Ministar ta ke nufi shi ne duk rana sai tallafin man fetur ya ci wa gwamnati N18.397bn.

Ana amfani da lita miliyan 65 kullum

A shekara mai zuwa, gwamnati tayi hasashen kullum za a rika shigo da lita kusan miliyan 65 na man fetur wanda asalin farashin litansa ya kai N448.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan aka yi lissafi da farashin da ake saidawa mutane fetur a kasuwa a kan N165, hakan na nufin gwamnati za ta cika gibin N283.2k da za a samu a lita.

'Yan Majalisa
'Yan Majalisa a wani zama Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

N6tr za su tafi a shekara daya

Sannan idan aka yi lissafin wannan kudi a yadda farashin Dalar Amurka take a yau, za a gane a duk shekara gwamnatin Buhari za ta rika batar da N6.5tr.

Sun ta rahoto Ministar ta na mai cewa daga Junairu zuwa Disamban shekara mai zuwa, za a kashe N6.715tr a wajen biyan tallafin fetur ga ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Majalisa Na Binciken Ministoci, An Bada Kwangilar Share Daji a Naira Biliyan 18.6

Ahmed ta fadawa ‘yan majalisa, a rabin shekara, za a ci 50% na wannan kudi, watau N3.375tr kenan. Wannan ne ya sa aka sa N3.357tn a cikin tsarin MTEF.

Kamar yadda Ministar tattalin tayi wa kwamitin bayani, tallafin shi ne bambancin kudin da ke tsakanin asalin farashin fetur da kuma farashin gidan mai.

Litar man fetur yana shigowa Najeriya a kan N448 ne, amma gwamnati ba ta so farashi ya tashi sosai a gidajen mai, don haka ta ke ragewa ‘yan kasa N283.

Kudiri ya zama doka

A tsarin mulki, kun ji labari idan ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya ko Sanatoci sun kammala yin kudiri, zai tsaya ne a kan teburin Shugaban Najeriya.

A shekaru bakwai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wasu kudirori da suka fito daga Majalisa, ya rattaba hannu, sun shiga cikin dokoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel