Kudirori 22 Daga Majalisa da Buhari Ya Sa Hannu tsakanin 2015 zuwa 2022

Kudirori 22 Daga Majalisa da Buhari Ya Sa Hannu tsakanin 2015 zuwa 2022

  • Daga zamansa shugaban Najeriya a 2015 zuwa yau, Mai girma Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wasu kudirorin ‘yan majalisar tarayya
  • Legit.ng ta bi jerin kudirorin da shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu, suka zama dokar kasa, wanda za su taimaka wajen kawo cigaban kasa
  • ‘Yan majalisa da Sanatoci su na sa ran kudirorin za su taimakawa gwamnati, wannan ne ya sa Buhari ya rattaba hannu, bai yi watsi da aikin na su ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kudirorin sun kunshi wadanda suka taba zabe, kawo karshen sata da ta’addanci. Cikin wanda ya fi shahara akwai dokar ba matasa damar shiga siyasa.

Ga kudirorin nan kamar yadda Fact.ng ta kawo su:

1. Dokar zabe ta shekarar 2022

2. Dokar haramta safarar kudi ta shekarar 2022 wanda ta shafe dokar Money Laundering (Prohibition) Act ta 2011

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

3. Dokar haramta ta’addanci ta shekarar 2022, wanda ta shafe dokar 2011

4. Dokar karbe dukiyar sata ta shekarar 2022

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

5. Dokar rabon kwangilolin karkashin kasa ta shekarar 2019

6. Dokar kafa hukumar AMCON ta shekarar 2019 da 2021

7. Dokar bada kariya wajen takara

8. Dokar kafa hukumar NCDC ta shekarar 2018

9. Dokar ba shukoki kariya ta shekarar 2021

10. Dokar taimakawa wajen yakar laifuffuka ta shekarar 2019

Buhari
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sauran kudirorinsu ne:

11. Dokar kafa asusun ‘yan sanda ta shekarar 2019

12. Dokar aikin ‘yan sanda ta shekarar 2020

13. Dokar aikin CAMA ta shekarar 2020

14. Dokar ba matasa damar shiga zabe ta shekarar 2018

15. Dokar aikin gidajen gyaran hali ta shekarar 2019

16. Dokar rage laifuffukan ruwa ta shekarar 2019

17. Dokar gashin-kan kudi ga majalisun dokoki da bangaren shari’an jihohi ta shekarar 2018

18. Dokar bankuna da kamfanonin kudi (BOFIA) ta shekarar 2020

Kara karanta wannan

Assha: Darajar Naira ta sake raguwa a kasuwar hada-hadar canjin kudade

19. Dokokin kudi na shekarun 2019 da 2020

20. Dokar hana nuna wariya ga masu nakasa ta shekarar 2018

21. Dokar CRA ta shekarar 2017

22. Dokar cinikin STMAA ta shekarar 2017

Za a canzawa Kaduna suna?

An yi shekaru ana kiran Kaduna da Jihar Kaduna, sai ga rahotanni na cewa 'Yan Majalisar Tarayya sun kai wa Shugaban kasa kudirin canjin suna.

Rade-radin da ake yi shi ne za a koma kiran Kaduna da jihar Zazzau, amma Sanata Uba Sani ya karyata wannan labari, ya fayyace gaskiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel