An yi Shahada Yayin da Ruwa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 50 a Kauyuka

An yi Shahada Yayin da Ruwa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 50 a Kauyuka

  • Ruwan sama ya yi karfi a Najeriya, har ya kashe mutum 50 a kananan hukumomi a Jigawa
  • Hukumar SEMA ta tabbatar da cewa daruruwan mutane sun rabu da gidajensu da suke nutse
  • Gwamnatin tarayya ta aika tawaga zuwa jihar an fara taimakawa wadanda abin ya shafa

Jigawa This Day tace Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa mutane 50 sun mutu a sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a wasu bangarorin jihar.

Shugaban hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa a jihar Jigawa, Sani Yusuf ya shaidawa manema labarai cewa ambaliyar ya taba mutane da-dama.

Sani Yusuf yace Bayin Allah rututu sun jikkata a sanadiyyar wannan musiba da ta auko. A halin yanzu, magidanta sun fake a makarantu da ofisoshi.

Rahoton yace a kauyen Balangu, gidaje akalla 237 suka nutse a ruwa, mutane hudu sun mutu. Maganar da ake yi, mutanen garin duk sun nemi mafaka.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Shahara a Sace Mata a Jihar Arewa

An yi babban rashi a Jigawa

Akwai wasu mutane shida da su ka mutu a ambaliyar a garin Kafin Hausa, sannan akwai wasu hudu dabam da aka iya tabbatar da labarin mutuwarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar tace zuwa ranar Asabar da ta wuce, an samu mutane bakwai ‘yan gida da suka cika.

Akwai mutane kashi-kashi da suke zaman wucin gadi a wasu wurare 11 da aka samar. A halin yanzu gwamnatin Jigawa ta ke daukar dawainiyar su.

Minista ta bada tallafi

Ministar walwala da bada agajin gaggawa ta kasa, Sadiya Farouq ta ziyarci wurin da abin ya faru, ta kuma raba kayan agaji a madadin gwamnatin tarayya.

Ma’aikatar kula da walwala da bada agaji na gaggawa ta tabbatar da wannan a shafin Twitter.

Sadiya
Sadiya Farouk tare da Sarkin Dutse a Hoto: @FMHDSD
Asali: Twitter

Kamar yadda gidan talabajin na CNN ya kawo rahoto, Ministar tace Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatarta ta taimaki wadanda ambaliyar ya taba.

Kara karanta wannan

Abuja: An kame wasu mutane 480 da ake zargin sun tsere daga magarkamar Kuje

Ba yau aka fara wannan ba

Ba wannan ne karon farko da ruwa ya kashe mutane a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ba. Hukumar NIMET tayi gargadin hakan zai faru.

A shekarar da ta wuce, gidajen mutane da yawa sun nutse a kauyen Guri da ruwan sama ya barke. Gwamnati tace dole magance lamarin zai dauki lokaci.

Binciken Magu

Ku na da labari cewa jiragen sama da otel da katafarun gidajen da Jami’an EFCC suka karbe daga hannun barayi duk sun yi kafa lokacin Ibrahim Magu.

Rahoton kwamitin PCARA ya nuna daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga Nuwamban 2018, jiragen ruwa sun nutse da kayan ciki, har yau shiru

Asali: Legit.ng

Online view pixel