Tunda Kunzo A Daura Kawai: Daga Zuwa Kai Gaisuwa, Iyaye Sun Nemi A Shafa Fatiha Kowa Ya Huta, Bidiyo

Tunda Kunzo A Daura Kawai: Daga Zuwa Kai Gaisuwa, Iyaye Sun Nemi A Shafa Fatiha Kowa Ya Huta, Bidiyo

  • Wasu abokai sun cika da mamaki bayan sun raka abokinsu gaishe da iyayen budurwarsa kawai sai aka nemi su kawo goro
  • Da isarsu gidan budurwar sai iyayen suka nemi su je su kawo goro da sadaki, suna dawowa kuwa aka shafa fatiha
  • Iyayen yarinyar sun kuma nemi angon ya zo ya dauki matarsa idan ya shirya bayan sun nemi ya yi komai iya karfinsa don arziki na Allah ne

Abuja - Mabiya shafin Twitter sun tofa albarkacin bakunansu bayan samun labarin wani aure da aka kulla ba tare da shiri ba kuma cikin sauki a karshen makon jiya.

Kamar yadda wani matashi mai suna Mista Bukhari Suwaid da shafin @suwaidybaba a Twitter ya bayyana, ya ce sun raka wani abokinsa gidan iyayen budurwar da yake nema da nufin gaisuwa.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

Sai dai da isarsu gidan, sai iyayen suka nemi su je su zo da goro inda suka shiga kaduwa matuka. Bayan nan sai suka yi kamar yadda aka umurce su inda suka siya goro suka kai tare da bayar da kudin sadaki gaba daya.

Amarya da ango
Tunda Kunzo A Daura Kawai: Daga Zuwa Kai Gaisuwa Iyaye Sun Nemi A Shafa Fatiha Kowa Ya Huta, Bidiyo Hoto: @suwaidybaba
Asali: Twitter

Ana haka kawai sai iyayen yarinyar suka ce kawai a daura auren tunda sun zo sannan suka umurci angon da ya zo ya tafi da amaryarsa idan ya shirya bayan sun ja hankalinsa a kan ya yi iya abun da zai iya daidai karfinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suwaid ya rubuta a shafinsa:

"Tunda kunzo a daura kawai" Na shaida wani daurin aure mafi sauki a jiya a Abuja. Kai musulunci sauki gare shi..
"Manta da auren soshiyal midiya, akwai iyayen kirki, Allah ya hada mu da su Kuma muma mu Zama mutannan kirki.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Koyawa Yan Mata Dabaru kan Yadda Za Su Tambayi Iyayensu Maza Kudi

"Ka Yi abun da zaka iya arziki na Allah, in ka shirya kazo ka dauki matarka.
"Daga Garki zuwa Sun City! Mun je da safe suka ce ku zo da goro! Mun kadu sosai, muka siyo goro da sadaki, bayan dan tattaunawa a takaice “Ina Walliyan sun? Baaba kawai sai aka daura, mun je da abokinmu a matsayin gwauro ya dawo da aure a kansa.
"Lamarin ya burge kowa! kamar a mafarki, yanayin ya kasance a tsanake, farin ciki da annashuwa."

Jama'a sun yi martani

Wannan al'amari ya burge mutane da dama inda suka ce suma suna fatan aurensu ya kasance cikin sauki haka.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@velli_jr ya ce:

"Allah sarki wannan labari ne mai dadi. Allah ya basu zaman lafia yayiwa auren su albarka ameen."

@mus_tukur ya yi martani:

"Irin wannan auren nake nema babu wahala babu al'ada addini kawai."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

@niimarh_tee ta ce:

"Abun ya yi kyau sosai MashaAllah. InshaAllah haka namu za ta kasance "tunda kunzo a daura"❣ aure cikin sauki da tarin albarka a ciki."

@RasheederhB ta ce:

"Allah basu zaman lafiya."

@ololade1_9 ta ce:

"Allah ya bada zaman lfy."

Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce

A wani labarin, wata matashiyar mata mai suna Misis Zanga a Twitter ta wallafa wasu hotuna don yabawa mijinta.

Matar a cikin wallafar da ta yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta, ta bayyana cewa mijinta yana taimakonta sosai da sosai.

Ta yi godiya ga Allah da ya bata mutumin a matsayin abokin rayuwa. A cikin hotunan, an gano mutumin ba riga yana taimakawa matar a cikin dakin girki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng