Yan Sanda Sun Daƙile Harin Yan Ta'adda a Jihar Katsina, Sun Kwato Dabbobi

Yan Sanda Sun Daƙile Harin Yan Ta'adda a Jihar Katsina, Sun Kwato Dabbobi

  • Yan ta'adda ya yawa sun sheƙa barzahu yayin da suka yi yunkurin kai hari kauyuka biyu a jihar Katsina
  • Hukumar yan sanda ta ce ta samu labarin zuwan yan ta'adda, nan take ta tura dakaru yankin ƙaramar hukumar Kurfi
  • Bayanai sun nuna cewa an yi artabu tsskanin jami'ai da yan ta'adda wanda ya yi sanadin kwato dabbobi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Ana fargabar dandazon yan bindiga sun sheƙa barzahu kuma wasu da dama sun jikkata bayan dakarun yan sanda sun daƙile yunkurin su na kai hari ƙauyukan Daudawa da Barkiya, ƙaramar hukumar Kurfi, Katsina.

Channels tv ta ruwaito cewa yayin artabu da yan bindigan, Gwarazan jami'an tsaron sun kwato Tinkiya 74 da Akuya 34 da Shanu guda biyu.

Dabbobin da yan sanda suka kwato.
Yan Sanda Sun Daƙile Harin Yan Ta'adda a Jihar Katsina, Sun Kwato Dabbobi Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Har Yanzun Akwai Sauran Fasinjojin Jirgin Ƙasa a Hannun Yan Ta'adda, Mamu Ya Faɗi Mummunan Halin Da Suke Ciki

"Hukumar yan sanda ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Litinin cewa yan ta'adda kusan 80 a kan Babura ɗauke da makamai sun kai farmaki kauyukan biyu," inji Kakakin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sanarwan, SP Isah ya ƙara da cewa bayan samun wannan bayanan, nan take hukumar ta tura tawaga ta musamman zuwa yankunan kuma suka yi musayar wuta da maharan.

Ya ce har yanzun tawagar yan sandan na can sun bazama cikin dazuka da nufin damƙo yan ta'addan da suka jikkata da ɗakko gawarwakin waɗan da suka kashe.

Kwamishina ya yaba da jajircewar yan sanda

Sanarwan ta ƙara da nuna cewa, kwamishinan yan sandan Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda, ya yaba da kokarin Jami'an na dakile mummunan harin yan ta'adda.

Ya kuma roki ɗaukacin al'umma su cigaba da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai a yaƙin da suke da yan ta'adda domin dawo da tabbataccen zaman lafiya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Shahara a Sace Mata a Jihar Arewa

A wani labarin kuma An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da mutane da ya shahara a sace mata a jihar Benuwai

Yan sanda sun yi ram da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane wanda ya shahara a sace mata a Makurdi, jihar Benuwai.

Gwamnatin jihar ta rushe gidan tsohon shugaban Alƙalai, wanda aka gano waɗan da ake zargin na mafaka a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel