Farashin Litar Man fetur Zai Zarce N400 Idan Peter Obi Ya Zama Shugaban kasa

Farashin Litar Man fetur Zai Zarce N400 Idan Peter Obi Ya Zama Shugaban kasa

  • ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party yace ba zai cigaba da tallafin mai ba
  • Peter Obi ya soki tsarin tallafin mai da Gwamnatin Muhammadu Buhari take biyan ‘yan kasuwa
  • Tsohon Gwamnan na Anambra yana so tattalin arzikin Najeriya ya daina dogara da man fetur

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, yace zai yi watsi da tsarin tallafin man fetur idan ya karbi mulkin kasar nan.

PM News tace Peter Obi wanda ya rika gujewa maganar tallafin man fetur a hirar da aka yi da shi a baya, ya fito karara, ya shaidawa Najeriya matsayarsa.

Da aka yi hira da shi a ranar Alhamis, 11 ga watan Agusta 2022, Obi ya tabbatar da cewa muddin ya karbi shugabancin kasar nan, zai janye tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

Jaridar tace an tattauna da ‘dan takarar a wajen wani taro da jam’iyyar Labour Party da kungiyar CPO suka shirya a dakin taro na ICC da ke garin Abuja.

Tallafin man fetur

‘Dan siyasar ya kira biyan tallafin man fetur da gwamnatin tarayya take yi da babban laifi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Muhammadu Buhari ta bar farashin man fetur a kasa da N200 saboda tsoron farashin kaya ya kara tashi. Obi da yake bayani a Twitter yace da sake.

Peter Obi
'Dan takaran Shugaban kasa, Peter Obi
Asali: UGC

A dalilin tsarin tallafin fetur, gwamnatin tarayya ta batar da fiye da Naira Tiriliyan 6.7. Idan aka daina biyan tallafin man fetur, duk lita zai haura N400.

“Dole mu dakatar da wannan barnar da sunan ‘tallafin man fetur’.
“Nan gaba da dole mu yi kokarin ganin yadda Najeriya za ta cigaba ba tare da man fetur ba.”

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Bankin Duniya ya yi Mummunan Hasashe a kan Halin Najeriya

- Peter Obi

Burin LP a Gwamnati

Idan jam’iyyar LP ta karbi mulki a 2023, tsohon gwamnan na Anambra yace babban burinsa shi ne samar da ayyukan yi, rage talauci da kawo zaman lafiya.

Gwamnatin Obi za ta habaka tattalin arzikin Najeriya, yake cewa babban kalubalen da ake fuskanta a kasar nan yau shi ne rashin shugabanni na kwarai.

Najeriya na cikin matsala

Duk da karancin kudin shiga da Najeriya ta ke fuskanta, mun ji labari cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na cigaba da biyan tallafin fetur har yau.

Bankin Duniya ya gargadi gwamnati cewa ya zama dole ta daina biyan tallafi, ta fadada haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel