Daga jin Mijinta zai kara aure, Matarsa ta banka ma gidansa wuta a Kebbi

Daga jin Mijinta zai kara aure, Matarsa ta banka ma gidansa wuta a Kebbi

Wata Mata mai suna Aisha ta banka ma gidan mijinta wuta sakamakon shirin kara aure da mijin nata ke da niyyar yi, duk kuwa da cewa watanninsu biyu kacal da aure, ini rahoton jaridar The Sun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Badariyya dake garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi, inda Aisha ta kona gidan mijinta Yunusa kurmus, saboda zai kara mata.

KU KARANTA: Yar aiki ta lakaɗa ma Uwardakinta dukan tsiya, ta shiga halin rai fakwai mutu fakwai

Rahotanni sun nuna cewar a watanni biyu kacal Amarya Aisha ya kwashe a gidan Angonta Yunusa, wanda ya aurota a watan Feburairu, jim kadan bayan mutuwar matarsa ta farko, don haka ta nuna masa bai dace ya karo mata tun yanzu ba, yayi wuri.

“A shekarar data gabata ne dai matar Yunusa ta farko ta rasu, inda ya auro Aisha a watan Feburairu, sai dai alamu sun nuna zaman nasu baya dadi tun bayan tarwarta, don haka ne Yunusa ya shirya kara aure, da ya sanar da Aisha niyyarsa shine ta harzuka, har ta babbaka masa gida a ranar Talata 6 ga watan Maris.” Inji wani makwabcinsu.

Makwabcin yace dayke dai babu wanda ya rasa rai a sakamakon wannan gobara, amma sun yi asarar dukkanin kayayyakinsu dake ciki, musamman na mijin, inda da kyar yan uwa da abokan arziki suka kashe wutar.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi Kaakakin rudunar Yansandan jihar Kebbi,DSP Suleiman Mustapha game da lamarin, sai yace basu samu bayani a hukumance ba daga wadanda abin ya shafa ko kuma daga ofishin Yansanda dake unguwar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: