Yan Bindiga Sun Sako Mutum 51 Da Suka Sace A Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Sako Mutum 51 Da Suka Sace A Jihar Kaduna

  • Masu Garkuwa da mutane sun sako kimanin mutum 51 da suka sace unguwar Millenium City da ke Jihar Kaduna bayan sun shafi makonni a hannun su
  • A watan Yunin da ta gabata ne wasu yan bindiga suka shiga gidajen mutane a Millinium city suka sace mutum 51
  • Mutane sun shaida cewa sai da aka biya yan bindiga kudin fansa na naira miliyan 2 kafin suka sako wadanda suka sace

Jihar Kaduna - Masu Garkuwa da mutane sun sako kimanin mutum 51 da suka sace unguwar Millenium City da ke Jihar Kaduna bayan sun shafi makonni a hannun su. Rahotan Aminiya

Rahotanni sun nuna cewa, sai da aka biya yan bindigan da suka yi garkuwa da mazauna Millinium City kudin fansa na naira miliyan 2 kafin suka sako su.

Kara karanta wannan

Yan ta'ada Sun Kashe Yan Banga Biyu Yayin da Suka Musu Kwantar Bauna a Abuja

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, babu wata fansa da aka biya masu garkuwa da mutanen da suka sako, kamar yadda jagoran rundunar hadin gwiwa da ke yankin, Uwaisu Yunusa ya tabbatar.

gunmen
Yan Bindiga Sun Sako Mutum 51 Da Suka Sace A Jihar Kaduna FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Wani mutum mazaunin Millinium City da ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa sai da aka biyan kudin fansa naira miliyan biyu kafin wadanda aka yi garkuwa da su suka shaki iskar yanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin ya bayyana cewa wadanda aka sace sun dawo gidane a ranar Asabar 13 Ga watan Augusta, kuma an yi maraba da dawowarsu yayin da fuskoki yake cike da farin ciki, sai dai abin takaici game da lamarin shine har yanzu akwai mutum daya a hannun yan bindigan.

Yan bindigan sun bukaci iyalan mutum daya da rage hannun su su siya musu babura guda biyu kafin su sako shi

Legit.NG ta rawaito labarin yadda masu garkuwa da mutane suka shiga gidajen mutane a Millinium city dake jihar Kaduna suka sace su, a karshen watan Yulin da ya gabata.

Kara karanta wannan

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

Abu Uku Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna - Isa Ashiru

A wani labari kuma, Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna Jam'iyyar PDP ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna. Rahoton BBC

Ashiru Kudan wanda ke takarar gwamnan jihar Kaduna karo na uku yace abun na farko da zai fara ba muhimmanci a jihar shine fannin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel