'Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 3 da Suka Shirya Sace Wata Mata a Osun
- Wasu tsageru sun yi yunkurin sace wata mata 'yar kasuwa, amma dubunsu ta cika yayin da suka shiga hannun 'yan sanda
- An kama 'yan ta'addan dauke da makamai, lamarin da yasa 'yan sanda zurfafa bincike don gano tushen laifin
- Ana yawan samun sace-sacen jama'a a jihohin Najeriya tare da karbar kudaden fansa a hannun dangin wadanda aka sace
Jihar Osun - Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, rundunar 'yan sandan jihar Osun sun yi nasarar cafke wasu mutum uku da suka yi yunkurin sace wata mata 'yar kasuwa.
'Yan ta'addan sun yi yunkurin sace matar mai suna Falilat Oyetunji, wacce aka fi sani da “Ero Arike” a garin Iragbiji.
Da yake bayyana faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yesima Opalola ta ce tsagerun kutsa gidan matar ne tare da kokarin daukar ta da karfi.
Da take ba da labarin yadda lamarin ya faru, Ms Opalola ta ce, 'yan sanda sun samu bayanan sirri, kuma sun kame 'yan ta'addan da misalin karfe 5:45 na yamma a ranar Litinin din da ta gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gabanin kame su, matar 'yar kasuwa ta kai rahoto ga 'yan sanda cewa ta samu labarin wani daga cikin tsoffin ma'aikatanta na shirya zuwa a sace ta, lamarin da yasa 'yan sanda mayar da hankali ga gidan matar.
A cewar wani yanki na sanarwar:
“Da sanyin safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Agusta, wani ya je ya sanar da Oyetunji, cewa wasu mutane karkashin jagorancin tsoho ma’aikacinta, wani Basiru daga Iragbiji ne suka shirya tare da kaddamar da yin garkuwa da ita."
Ta kuma bayyana, bayan da Oyetunji ta sanar da 'yan sanda, tuni aka tura jami'an dakile garkuwa da mutane domin zuba ido da kuma kwamushe tsagerun, kamar yadda Daily Sun ta ruwaito.
Ta kara da cewa:
"An samu nasarar kwato bindigogin guda biyu, doguwar wuka daya da wukar Jack daya daga hannun wadanda ake zargin."
A rahoton, an ce daya daga cikin 'yan ta'addan ya raunata a ciki da wuka, kuma yanzu haka an mika shi ga wani asibiti domin karbar kulawar likita.
Ta ce, duk da haka, ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Jihar Neja: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Kodinetan Hukumar FIRS, Sun Sace Mutum 3
A wani labarin, rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe Kodinetan Hukumar Haraji ta Kasa (FIRS) mai kula da jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi, Alhaji Muhammad Kudu Adamu a daren Lahadi a unguwar Saminaka da ke kan hanyar Lapai-Lambata a jihar Neja.
Wani abokin marigayin mai suna Dokta Zubairu Ibrahim ya shaida wa Daily Trust cewa yana dawowa ne daga garin Lafiagi da ke Jihar Kwara, inda ya je gaishe da ‘yan uwansa da suka dawo daga aikin hajji lokacin da ya gamu da 'yan bindigan.
Ya ce Adamu da wasu mutane uku da ke cikin motar sun yi taho-mu-gama da ‘yan bindigar da suka yi harbin kan mai uwa da wabi ga motarsu, lamarin da ya kai ga rasa rai.
Asali: Legit.ng