Musiba ta Sake Aukawa Dattijon Arewa, An Sace Surukarsa da Yara a Sabon Hari

Musiba ta Sake Aukawa Dattijon Arewa, An Sace Surukarsa da Yara a Sabon Hari

  • ‘Yan bindiga sun dura kauyen Yakawada a Kaduna, sun yi nasarar yin ta’adi cikin duhun dare
  • Wasu daga cikin Surukan Ango Abdullahi suna cikin wadanda Miyagun suka yi garkuwa da su
  • Ba wannan ne karo na farko da aka kai hari a karamar hukumar Giwa, aka kashe Bayin Allah ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - A ranar Laraba, 10 ga watan Agusta 2022, Farfesa Ango Abdullahi ya shaida cewa ‘yan bindiga sun dauke surukarsa da kuma ‘ya ‘yan ta.

Dattijon ya shaidawa Daily Trust cewa matar ‘dan sa tana cikin wadanda ‘yan bindiga suka dauke tare da iyalinta a lokacin da aka kai hari a yau.

“Diyata Ramatu Samaila tana cikin wadanda aka dauke, tare da yaranta hudu. Mai dakin surukina ce, wanda shi ne Mai unguwar kauyen Yakawada.”

- Ango Abdullahi

Kara karanta wannan

Duk bula ce: Ainihin Abin da ya sa Ake Barazanar Sauke Buhari inji Dan Majalisa

'Yan bindiga sun je gidan Mai unguwa

Daily Trust tace da isarsu kauyen, ‘yan bindigan sun dura gidan Mai unguwar Yakawada ne, Alhaji Rilwanu Saidu, suka dauke wasu iyalinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan iyalin Rilwanu Saidu da aka yi garkuwa da su, ‘yan bindigan sun dauke wasu daga cikin makwabtan wannan Bawan Allah, suka yi gaba da su.

Majiyar Daily Trust tace an dauke wani Abubakar Mijinyawa tare da matansa biyu – Aisha da Hajara, wadanda dukkaninsu suke goyon kananan yara.

'Yan bindiga
'Yan bindiga a Zamfara Hoto: www.cfr.org
Asali: UGC

Sannan ‘yan bindigan sun harbe wani mai gadi, Aminu Lawal a lokacin da aka kai harin. Mutane uku da suka samu rauni suna asibitin ABUTH a Shika.

Ana kallo suna shiga jeji

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘yan bindiga sun shiga wannan kauye na Yakawada da ke karamar hukumar Giwa cikin tsakar daren Laraba.

Kara karanta wannan

Babban kamu: Mata 7 da ke kai wa Boko Haram kayan abinci sun shiga hannu a Borno

Malam Bangis Yakawada ya shaida cewa miyagun sun dauki kusan awa biyu su na ta’adi ba tare da hukuma ta kawowa mutanen kauyen wani agaji ba.

A cewar matashin, mutanen gari sun ga ‘yan bindigan da safe suna tafiya da mutanen da suka yi garkuwa da su, sun kama hanyar shiga da su jeji.

Musiba a kan musiba

Farfesa Ango Abdullahi wanda shi ne shugaban kungiyar NEF ta dattawan Arewa ya fito daga wannan yanki ne a Kaduna, shi ne Magajin Rafin Zazzau.

Wata kusan daya kenan da ‘yan bindiga suka saki Sadiq Ango Abdullahi, wanda yana cikin fasinjoji 60 da aka dauke a jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Kafin nan kuma, a karshen watan Yunin 2022, Farfesan ya rasa babban ‘dansa a Duniya, Malam Isa Ango Abdullahi, wani ma'aikacin NIA a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel