Kaduna 2023 : Tsohon shugaban Kungiyar Sokapu ya Zama Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar Labour Party

Kaduna 2023 : Tsohon shugaban Kungiyar Sokapu ya Zama Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar Labour Party

  • Dan gwagwarmaya kuma tsohon shugaban Kungiyar Kudancin Kaduna Sokapu ya Zama Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar Labour Party
  • Jonathan Asake ya Dauki Alhaji Bashir Idris Aliyu Zangon Aya, A matsayin dan takarar mataimakin gwamana
  • Asake ya ce Jam'iyyar Labour Party ta kudirin aniyar kwace mulki daga hannun APC dan dawo wa jihar kaduna kima da martabar da tske dashi a da41

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - Jam’iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Kaduna ta gudanar da zaben fidda gwani inda tsohon shugaban kungiyar Kudancin Kaduna ta kasa (SOKAPU), Hon. Jonathan Asake, ya fito a matsayin dan takararta na gwamna a zaben 2023. Rahoton VANGUARD

Jonathan Asake ya dauki tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kaduna kuma tsohon kwamishinan ayyuka Alhaji Bashir Idris Aliyu Zangon Aya, a matsayin abokin takarar sa.

Kara karanta wannan

Rikici: Kiristocin APC a Arewa sun ta da hankali, dole a kwace tikitin Shettima a ba su

Jonathan Asake, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa zai shiga takarar gwamna jihar Kaduna ne don amsa kiran magoya bayan sa.

Asake
Kaduna 2023 : Tsohon shugaban Kungiyar Sokapu ya Zama Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar Labour Party FOTO VANGUARD
Asali: UGC

Yayin da yake mika godiyar sa ga mambobin Labour Party da suka fito daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, Asake ya ce nasarar sa a zaben fidda gwani ya tabbatar musu da cewa ya amsa kiran da al’ummar jihar Kaduna suka yi mishi na tsayawa takara gwamna a zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin Jonathan Asake yace Jam'iyyar LP ta kuduri aniyar kwace mulki daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) domin dawo da kima da martabar da jihar Kaduna take dashi a baya.

Daga karshe, Jonathan Asake ya gode wa wakilai da shugabannin jam'iyyar LP, inda yayi musu alkawarin cewa idan ya zama gwamna zai yi aiki da kowa da kowa ba tare da la'akari da inda suka fito da kuma addinin su.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi-Musulmi: Paparoma bai ce na yi kuskuren marawa Tinubu da Shettima baya ba, inji Lalong

An Shiga Yanayi Rudani a Jihar Jigawa Yayin da Yansanda Suka Sako mutumin da ake Zargi da laifin Kisan Kai

A wani labari kuma, Yan uwan wani mutum da ake zargin an kashe shi a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a ranar Larabar da ta gabata, sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakin wanda ake zargin yayi kisan da ‘yan sanda suka yi. Rahoton Premium Times

Wanda aka kashe, Yusuf Umar, ya rasu ne a ranar 21 ga Yuli, 2022 a Asibitin Aminu dake Kano, kwanaki 18 bayan an kai masa hari a kasuwar karkarar Amaguwa da ke yankin karamar hukumar Ringim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel