Sakon Maulidi: Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci musulmi su hada kansu
- Shaihin Malami Sheikh Dahiru Bauchi yayi kira ga dukkan musulmin Najeriya su kaunaci juna duk da banbancin da ke tsakanin su
- Malamin yayi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Maulidi da ya bayyana wa manema labarai da suka ziyarce sa a gidansa da ke Bauchi
- Malamin ya shawarci iyaye su gina yaransu kan koyarwa irin ta addinin musulunci kuma yayi addu'an cigaba ga Najeriya da fatan Alheri ga Shuga Muhammadu Buhari
Shahararen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga al'ummar musulmi su rungumi kauna, hakuri da juriya a harkokinsu na yau da kullum kamar yadda Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.
Yayi wannan kiran ne a ranar Juma'a a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidan sa da ke garin Bauchi a cikin sakonin sa na murnar zagayowar ranar haihuwa fiyayen halita, Annabi Muhammad (SAW).
Shaihin malamin yace Maulidi lokaci ne da musulmi ya kamata su kusanci Allah ta hanyar nuna kauna ga Manzo kuma Annabin sa Muhammad (SAW), Ya kuma yi kira da daukakin al'ummar musulmi su kaunaci juna duk da banbance-banbancen da ke tsakanin su domin ciyar da addinin musulunci gaba.
DUBA WANNAN: Kada ku hana sana'ar kabu-kabu - Ameachi ya roki Jihohi
Ya kuma yi kira ga iyaye su dage wajen tura yaran su makarantar Islamiyya domin su samu tarbiyya mai kyau kuma su rika koyar dasu tarihin manzon Allah domin su amfana da darusan da ke ciki.
Malamin yayi kira ga gwamnatocin Tarayya da Jihohi su bullo da shirye-shirye da zasu saukaka rayuwar talaka musamman bayan matsin tattalin arziki da kasar ta fuskanta a farkon shekarar nan.
Daga karshe Sheikh Dahiru Bauchi yayi kira ga yan Najeriya su dage da addu'o'i domin kallubalen da Najeriya ke fuskanta kuma yayi fatan alheri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng