Gwamnoni Sun Bukaci Buhari Ya Dauki Matakai 33 Don Ceto Tattalin Arzikin Najeriya

Gwamnoni Sun Bukaci Buhari Ya Dauki Matakai 33 Don Ceto Tattalin Arzikin Najeriya

Gwamnonin Najeriya sun shawarci gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta ɗauki wasu matakai cikin gaggawa a wani yunkurin rage wahalhalun kasafin kuɗi da ceto ƙasa daga durkushewar tattalin arziki

Gwamnonin sun gabatar da matakan yayin gana wa da shugaba Buhari a watan da ya shuɗe, rahoton Premium Times ya tabbatar daga wata majiya da bat da ikom faɗin abinda aka tattauna a taron.

Jaridar ta rahoto cewa gwamnonin sun shawarci gwamnatin tarayya da ta yi wa ma'aikatan da suka zarce shekara 50 tayin ritaya a shekara ɗaya domin su aje aiki.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan yanayin taɓarɓaarewar tattalin arziki da kuma yadda yake shafar Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Shugaba Buhari da gwamnoni.
Gwamnoni Sun Bukaci Buhari Ya Dauki Matakai 33 Don Ceto Tattalin Arzikin Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A farkon makon nan, wani bincike da Premium Times ta gudanar kan asusun ajiya na Najeriya ya nuna cewa adadin da ke ciki ya koma dala biliyan $15 bn, ƙaasa sosai daga dala biliyan $36 bn da Babban Bankin Najeriya ya yi ikirari.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duba da Tiriliyan N1.5trn da Najeriya ke kashe wa wajen shigo da kayayyaki daga waje, asusun mai kunshe da $15bn ba zai ɗauki nauyin abinda ya wuce watanni huɗu ba

Haka nan wasu alamun baya bayan nan sun nuna cewa Najeriya ta talauce kasancewar bashin da ke kanta ya zarce kuɗaɗen da take samu.

A bayanan rahoton aiki da kasafin kuɗin 2022 daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, Najeriya na samun kuɗin shiga tiriliyan N1.63trn, yayin daa bashi ya kai Tiriliyan N1.94, banbancin sama da biliyan N300bn.

Gwamnonin sun shawarci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ɗauki matakai kamar haka:

Rage kashe-kashen FG da kuɗin da zasu ragu a cikin Baka

1. Cire Tallafin man fetur (6 zuwa 7 Tiriliyan).

2. Cire Kamfanin man fetur na ƙasa NNPC daga Asusun tarayya (Biliyan N300bn)

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: A Karon Farko, Gwamna Wike da Atiku Abubakar Sun Sa Labule A Gidan Wani Tsohon Minista

3. Rage yawan kasafin kuɗin da ake ware wa tsarin jin kai SIP da tsarin yaƙar talauci zuwa biliyan N200bn (Biliyan N570bn)

4. Dakatar da kuɗin da ake cire wa na kwansutushin daga asusun tattara kuɗaɗen shiga FAAC (Biliyan N100bn).

5. Rage yawan kuɗaɗen SWV na SDG da kuɗin ayyukan mazaɓu na majalisa (Biliyan N300bn)

6. Rage ayyuka masu kama ɗaya misali tsarukan ba da tallafi (Biliyan N100m)

7. Rage kaso ɗaya daga abinda ake ba NASENI ya koma 0.2%. A gyara dokar a kundin dokokin kudi 2022.

Rage kudin da ake kashe wa a ma'aikatu

8. Baiwa ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka haura shekara 50 tayin kunshin ritaya domin su bar aiki (Biliyan N350bn), daga bisani a ɗauki kananan ma'aikata, matasa masu kwarewar fasahar zamani da mata.

9. Fara aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye (Tiriliyan ɗaya).

10. Gaggauta siyar da kadarorin gwamnati da basu taɓuka komai (Biliyoyin Naira).

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata Dake Gadon Rashin Lafiya a Zariya, Jihar Kaduna

11. Sake nazari kan tsarin MTEF 2023-2025 da sabunta shi dai-dai da kashe kuɗin gwamnati da kokarin gwamnati na farfaɗo da kasafi.

12. A sake duba shirin ƙarin Albashi na ƙaso 22 a shekarar 2023.

13. Rage rashin isar kasafin kudi da abinda bai zarce kashi 2 na GDP ba a 2023-2025.

14. Dakatar da fita kasashen waje na ma'aikatu da suka haɗa da CBN, FIRS, NPA, NIMASA da NCC na aƙalla shekara ɗaya.

15. Ma'aikatar harkokin waje ta nemi ofisoshin jakadanci ƙasashe su dakatar da baiwa jami'an FG da iyalansu Visa har sai fadar shugaban ƙasa ta amince.

16. Canza tsarin biyan haraji.

17. Tare da kirkirar kaso uku na harajin shiga ga gwamnatin tarayya, ya kamata a soke harajin PIA na matakin jiha

18. Harajin sayar da kaya (Kaso 10% bai ɗaya) ya kamata ya hau kan kowace jiha har da Abuja.

19. A ƙara harajin VAT zuwa kashi 10% tare da sa lokacin da za'a ɗaga shi zuwa tsakankanin 15% da 20%.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Bayyana Shirinta Na Dawo Da Zaman Lafiya Gabanin Zaben 2023

20. Sake gabatar da kudirin canza VAT zuwa jerin waje wato 'Exclusive List' tare da tabbatar da ya tsallake ko ina.

21. Dakatar da CBN daga samar da kuɗaɗen kashewa ga FG.

22. Kirkiro da biyan harajin kaso 3% kan kowane ɗan Najeriya da ke samun sama da N30,000 a wata (biliyan N100bn)

23. Duk wanda ke samun ƙasa da N30,000 a wata ma'aikaci ko mara aiki, manoma da yan kasuwa su rinƙa biyan harajin N100 duk wata.

24. Kamfanonin sadarwa da hukumar NIMC su haɗa kai wajen zare waɗan nan kudin daga layukan wayan Yan Najeriya.

25. Maida cibiyar tattara haraji baki ɗaya a hukuma ɗaya, FIRS, yayin da kwastam da sauran hukumomi su koma tantance wa da kayyade abinda za'a biya.

26. Ƙara inganta ɗanyen man da ake hakowa a teku.

27. Warware batutuwan da suka shafi mallakin iskar gas misali Nnwa-Doro, OML 129, hakan zai taimakawa Najeriya ta yi amfani da bukatar Gas a Turai.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Shugaban Makarantar Gwamnatin Tarayya A Kaduna, Sun Kashe Rai

28. Samar wa dama kawo karshen matsalolin fasa bututu irin su Bonga SW (Shell), Preweoi (Total), Zabazaba (ENI) and Owowo (Exxon).

29. Taimaka wa da ƙara kwarin guiwa wajen kammala matatar man Ɗangote da wuri domin rage yawan canza kudin kasashen waje.

Abinda ya shafi CBN

30. A sake zubin Bankin Manoma, Bankin yan kasuwa da Bankunan cigaba na Najeriya.

31. Kuɗaɗen da ke Bankin NIRSAL waɗan da CBN ke juyawa a maida su bankin cigaba.

32. A umarci CBN ya maida hankali kan muhimman aikin da ke kansa da suka hada da jagorancin canjin kudi, adadin kuɗin riba, manufar tashin farashi. Haka kuma a hana CBN ya dena gasa da sauran bankuna.

33. A kawo ƙarshen shiga daa bayar da tallafin da CBN ke yi a wasu ma'aikatu. Hukumomin da abun ya shafa kuma a sake musu zubi don gudanar da ayyukan su.

A wani labarin kuma Yan kasuwa sun koka cewa duk da akwai Fetur a Najeriya da yuwuwar a fara dogon layi a Abuja nan gaba kaɗan

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Jihar Shugaban Ƙasa, Sun Ci Karen Su Babu Babbaka a Garuruwa uku

Da yuwuwar nan ba da jimawa za'a sake shiga wahalhalun ƙarancin Man Fetur a birnin tarayya Abuja.

Wasu bayanai daga ƙungiyoyin yan kasuwa sun nuna cewa Direbobin sun ƙi ɗaukar Man saboda ɓacin hanyar Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel