Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

  • Yan bindiga sun farmaki kauyen Tashan Buja da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina
  • Bayanai sun nuna maharan sun yi garkuwa da wasu mutane shida ciki harda matar aure da danta
  • Tsagerun masu garkuwa da mutanen sun kira mijin matar auren da ke ciki, inda suka bukaci a biya kudin fansa

Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a Tashan Buja da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 12:30 na tsakar daren Juma’a ba tare da harbi ba sannan suka dauke wata matar aure, danta da wasu mutane shida, jaridar Leadership ta rahoto.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Katsina Post ta nakalto wata majiya mai tushe, wanda mazaunin garin ne, yana cewa:

“Yanzu haka daga gidan mutumin da yan bindiga suka sace matarsa da dansa a daren jiya nake. Mutane sun ga maharan sun doshi jeji tare da wasu mutane hudu, inda ya zama shida suka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Gano Gawarwakin Mutum 26 Da Suka Nutse A Ruwa Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sun shigo garin da misalin karfe 12:30 na tsakar dare, sun aiwatar da ta’asarsu shiru ba tare da harbi da zai nuna kasancewarsu a wajen ba.
“Yan bindigar sun zanta da Mista Musa Shaun, mijin matar da aka sace, inda suka bukaci a biya naira miliyan 50 a matsayin kudin fansarsu.”

Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Babban Basarake A Jihar Taraba

A wani labarin, mun ji cewa wasu mutane dauke da bindigu waɗan da ake zargin 'Yan bindiga ne sun halaka Ibrahim Yamusa, basaraken masarautar Yakuben, cikin karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Channels Tv ta samo cewa 'yan bindigan sun halaka matukin sa wanda kuma ya kasance dan sa ne.

Kafin halaka su, 'yan bindigan sun sace basaraken da dan na sa a ranar Alhamis, a wani kwanton bauna da su ka kai musu akan hanyar su ta dawowa daga Takum.

Kara karanta wannan

Duk sace N109bn na kasa, kotu ta ba da belin akanta janar da shugaba Buhari ya dakatar

Asali: Legit.ng

Online view pixel