PDP Ta Dage Taronta Na NEC da Majalissar Wakilai Yayin da Rikicin Tsakanin Atiku da Wike Ke Kara Ruruwa

PDP Ta Dage Taronta Na NEC da Majalissar Wakilai Yayin da Rikicin Tsakanin Atiku da Wike Ke Kara Ruruwa

  • Jam'iyyar PDP na kara dagulewa, ta age wasu taruka guda biyu da za ta yi a makon nan masu muhimmanci
  • Ana ta kai ruwa rana tsakanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP da kuma gwamnan Ribas Wike
  • Atiku ya zabi gwamnan jihar Delta Okowa a matsayin abokin takara, lamarin da ya kunno wutar rikici a inuwar lemar PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jam’iyyar PDP ta dage taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ‘yan majalisar wakilai na kasa, biyo bayan dambarwar da ta dade tsakanin dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ke kara dagulewa.

A tun da farko dai an shirya gudanar da tarukan gabobi biyu masu muhimmancin ne a gobe Laraba da kuma Alhamis, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Majalisa za ta titsiye ministar kudi kan batun kudaden tallafin man fetur

Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar, ta ce an dage zaman ne saboda wasu abubuwan da suka bullo da ba a yi tsammani ba.

Rikicin PDP na kara ta'adda tsakanin Wike da Atiku
PDP Ta Dage Taronta Na NEC da Majalissar Wakilai Yayin da Rikicin Tsakanin Atiku da Wike Ke Kara Ruruwa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce nan gaba kadan za a sanar da sabbin ranakun taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa sakataren bai bayyana dalilin da ya sa aka dage zaman ba, majiyoyin jam’iyyar sun ce sun yanke hakan ne sakamakon matsaya mai tsauri da gwamnan jihar Ribas ya dauka a yunkurin sulhunsu da Atiku.

Daga cikin wasu bukatu da yawa, sansanin na Wike ya yi kira ga shugaban PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu da ya sauka daga mukaminsa ya bar daya daga cikin mataimakansa daga Kudu ya karbi mukamin.

Sun nemi wannar kujerar ne ganin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da shugaban kwamitin amintattu (BoT) da shugaban kasa jam'iyyar duk ‘yan Arewa ne.

Kara karanta wannan

Dan majalisan da ya gudu a APC saboda neman kujerar takara a PDP ya dawo, ya rasa tikiti

Wata majiya ta ce goron gayyatar da Wike ya yi wa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu zuwa kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ta ruguza wasu fuka-fukai daga manyan jam’iyyar PDP.

A cewar majiyar, shawarar da Wike ya yanke na gayyatar gwamnan na Legas, wanda dan jam’iyyar APC ne, zuwa kaddamar da ayyuka a jihar da ke karkashin jam’iyyar PDP, ya faru ne saboda nuna rashin amincewa da shugabancin jam’iyyar.

Yadda Wike yake shigewa jiga-jigan APC, makusanta Tinubu

A ranar 8 ga watan Yuli ne Wike ya karbi bakuncin gwamnonin APC uku - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanwo-Olu - kwanaki kadan bayan Atiku ya bayyana gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.

An ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ba su ji dadin yadda gwamnan na Ribas yake shigewa jiga-jigan jam’iyyar APC ba, musamman makusantan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

Rahotanni sun ce Wike ya samu goyon bayan wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da kuma kungiyoyi masu karfi domin ya samu kujerar mataimakin Atiku, inji The Nation.

Sai dai Atiku a ranar 16 ga watan Yuni, ya bayyana Okowa a matsayin mataimakinsa, sabanin shawarar da kwamitin tantancewa ya bayar, wanda ya ce Wike ne zai zama mataimakinsa.

Atiku ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar PDP a ranar 29 ga watan Mayu da kuri'u 371 yayin da Wike ya zo na biyu da kuri'u 237.

Ko ba Wike Zan iya Nasara a Zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

A wani labarin, tahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ganawar da Atiku Abubakar ya yi da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ta gaza kawo wani sauyi a rikicin da ke tsakaninsu.

A cewar rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da gwamnan a gaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

An ce tsohon ministan yada labarai da al’adu, Farfesa Jerry Gana ne ya shirya taron a gidansa. A wani taro da mambobin BoT na PDP a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, Atiku ya bayyana cewa PDP za ta iya lashe zaben badi ba tare da kuri’un jihar Ribas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.