Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar

  • Jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta bayyana jewa ta gamsu da salon jagorancin shugabanta Iyorchia Ayu don haka ba zai yi murabus ba
  • Jam'iyyar ta kuma ce kwamitin amintattu ta kafa wani kwamitin da zai warware matsalolin da ke jam'iyyar musamman tsakanin magoya bayan Wike da Atiku Abubakar
  • Wike da magoya bayansa sun fusata ne tun bayan da ya sha kaye hannan Atiky a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar kuma ba a dauke shi matsayin mataimaki ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta jaddada cewa ta gamsu da kamun ludayin shugabanta na kasa Iyorchia Ayu, Premium Times ta rahoto.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba ne ya sanar da hakan a Abuja a ranar Talata bayan taron da aka yi da kwamitin ayyuka, NWC, da tsaffin sakatarorin watsa labarai na kasa, jiha da yanki.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Ayu da jiga-jigan PDP.
Kuri'ar Gamsuwa: PDP Ta Aminta Da Salon Jagorancin Ayu Duk Da Rikicin Jam'iyyar. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Kuri'ar 'gamsuwa' da aka yi wa shugaban jam'iyyar yana zuwa ne a lokacin da rikicin jam'iyyar ke ƙara ƙamari har wasu ne neman ya yi murabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta rahoto yadda Nyesom Wike gwamnan jihar Rivers ya gana da wasu gwamnoni da shugabannin PDP a ranar Lahadi.

Wike, wanda ke fushi da jam'iyyar tun bayan kayen da ya sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa da rashin zabensa a matsayin mataimaki, da farko, ya ki yarda ya gana da Atiku Abubakar.

Mr Wike da magoya bayansa na son a tsige Mr Ayu daga shugabancin PDP. Suna kuma son a yi garambawul a kwamitin ayyuka na jam'iyyar wato NWC.

Kwamitin amintattu na jam'iyyar, BoT, a ranar Laraba, ta kafa kwamiti don sulhunta bangarorin biyu kuma a ranar Alhamis, Wike da Atiku sun yi ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Kuri'ar gamsuwa kan Atiku da Ayu

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a karshen taron, Mr Ologunagba ya ce wadanda suka hallarci taron sun gamsu cewa Ayu da NWC su cigaba da jagorancin jam'iyyar kuma sun yi imanin Atiku zai ceto jam'iyyar ya sauya akalarta ya sake gina kasa har kasashen waje su fara ganin Najeriya da daraja.

Jam'iyyar a karkashin jagorancin Atiku za ta iya kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya kuma ta gina tattalin arzikin kasar, in ji shi.

Da aka masa tambaya kan halin da aka ciki a batun kwamitin sulhun da BoT ta kafa, ya ce suna kyautata zaton za a warware matsalolin.

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

A wani rahoton, kun ji cewa a yammacin Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022 ne aka yi wani zama domin ayi sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Tsigaggen mataimakin gwamnan PDP ya ja zuga, masoyansa sun koma APC

Premium Times ta fitar da rahoto na musamman da ke cewa an yi wannan zama ne a gidan tsohon Ministan tarayya a Najeriya, Farfesa Jerry Gana.

Haduwar ‘dan takaran shugaban kasar da gwamnan na Ribas na zuwa ne jim kadan bayan ‘yan majalisar amintattu na BoT sun yi wani zama a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel