Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

  • Wata budurwa ta janyo cece-kuce a soshiyal midiya bayan bidiyonta ya bayyana inda take bai wa saurayinta kyautar PS5
  • A bidiyon wanda yanzu ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani masu yawa, an ga budurwar ta taho da kyautar ta ba-zata
  • Matashin ya matukar shan mamaki saboda ya dade yana son siyawa kansa PS5 da dadewa amma sai gashi ya samu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani matashi da burinsa shine ya mallaki PS5 ya cika bayan budurwarsa ta cika masa wannan burin a kwanakin nan.

Budurwa ta yi kokari inda har ta siya masa sabuwar na'urar wasan ta PS5 kuma ta bashi a lokacin da bai taba zato ko tsammani ba.

Budurwa ta bashi kyauta
Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal. Hoto daga @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Abu ne da ya dade yana so

Babu zato balle tsammani budurwar ta shiga gidan tare da mika wa saurayin nata, lamarin da ya faranta masa rai matukar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mai siyar da tsire ya zama ɗan gaye bayan kamfani sun ɗauke shi talla

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin ya matukar razana yayin da ya dinga kallon kyautar mai muhimmanci, daga bisani ya zauna tare da boye fuskarsa a tafukan hannunsa cike da mamaki.

Bidiyon ya janyo tsokaci mabanbanta

Bidiyon da ya yadu ya janyo maganganun jama'a a soshiyal midiya. Wasu sun ce akwai wuya samun budurwa mai irin wannan zuciyar.

Amma wasu mata a Instagram da suka bayyana tunaninsu kan bidiyon, sun ce zasu iya irin haka ga mazan da suke kauna idan suna da hali.

Ga bidiyon:

@obaksolo yace: "Ubangiji na yin son jai wurin raba irin wannan soyayyar. Soyayya tana da dadi. Gareku masu neman soyayya, muna muku fatan alheri."
@wrldprincecharming: "Wasu matan sun buga tsaki tare da ficewa daga zauren tattaunawar."
@_ugez yace: "Mtswww... Mu mayar da hankali kan zabe da Allah."
@mrs_bybah: "Zan iya yin hakan idan ina da kudin."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci

@badboysammyx yace: "Matan Najeriya sun fice daga zauren tare da toshe shugabar."

Kano: Wurin rige-rigen shiga gaban mota, amarya ta sumar da uwargida, alkali ya aikata gidan yari

A wani labari na daban, Alkali ya aike da amarya gidan gyaran hali bayan da ta sumar da kishiyarta yayin da suke rige-rigen shiga gaban motar mijinsu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, lamarin ya auku a Kano ne a satin da ya wuce. Uwargida ta sanar da kotun shari'ar dake Kofar Kudun gidan Sarki a gaban Alkali Ibrahim Sarki Yola cewa, kishiyarta ta lakada mata duka.

Uwargidan dake kara tace bata cika lafiya ba, lamarin da yasa mijinsu ya aiko da mota a kai ta asibiti saboda ba za ta iya tuka motarta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel