Kano: Wurin rige-rigen shiga gaban mota, amarya ta sumar da uwargida, alkali ya aikata gidan yari

Kano: Wurin rige-rigen shiga gaban mota, amarya ta sumar da uwargida, alkali ya aikata gidan yari

  • Alkalin kotun shari'ar Musulunci dake Kano ya aike da wata amarya gidan yari kan zarginta da sumar da uwargidanta
  • Kamar yadda uwargida tayi bayani, mijinsu ya aiko da mota a kai ta asibiti amma amarya tace sai ta fito daga gidan gaba inda ta ke zaune
  • Daga nan ne amaryar ta lakada mata duka har ta kai ta da suma aka kwasheta magashiyyan rai a hannun Allah sai asibiti

Kano - Alkali ya aike da amarya gidan gyaran hali bayan da ta sumar da kishiyarta yayin da suke rige-rigen shiga gaban motar mijinsu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, lamarin ya auku a Kano ne a satin da ya wuce. Uwargida ta sanar da kotun shari'ar dake Kofar Kudun gidan Sarki a gaban Alkali Ibrahim Sarki Yola cewa, kishiyarta ta lakada mata duka.

Kara karanta wannan

Mijina Raggo Ne, Ya Boye A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shigo Gidanmu, Mata Mai Neman Saki

AMarya da uwagida
Kano: Wurin rige-rigen shiga gaban mota, amarya ta sumar da uwargida, alkali ya aikata gidan yari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Uwargidan dake kara tace bata cika lafiya ba, lamarin da yasa mijinsu ya aiko da mota a kai ta asibiti saboda ba za ta iya tuka motarta ba.

Uwargida ta bayyana cewa, tana shiga motar ne amarya ta rike kofa tana ce mata ta fito, inda ita kuwa tace ba za ta fito ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kafin kace wannan, sai na ji an make ni a goshi na. A take na fadi a sume kuma aka garzaya da ni asibiti," cewar Uwargida.

A bangaren amarya kuwa, ta dire tace bata aikata hakan ba.

Mai shari'a Ibrahim Yola ya aike da amaryar gidan gyaran hali inda ya dage sauraron karar har zuwa sati na gaba.

Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci

A wani labari na daban, wata budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta bayyana kalaman karshe na mamacin wanda tace da kanshi ya bayyana mata.

Kara karanta wannan

Na Rabu Da Mijina Saboda Ya Boya a Ban Daki Ya Barni A Hannun Yan Fashi Da Makami

A wani bidiyo da @natnats41 ta saka a TikTok, budurwar ta haye mumbari kuma tayi jawabi ga masu makokin mutuwar.

Ta fara ne ta hanyar jero sunayen 'ya'yan mamacin sannan ta fallasa wacce take zargin ta halaka shi.

Budurwar da tayi ikirarin cewa ta kwashe kwanaki uku da mamacin inda ta tambaye shi abinda ya kai shi kwance kuma kai tsaye ya bayyana abinda ke niyyar aika shi barzahu.

Ta kara da bayyana cewa, mamacin mai suna Paul ya sanar da ita cewa matarsa ce take yi masa barbaden wasu abubuwa a cikin abinci.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel