EFCC Ta Gayyaci Hadimar Ministan Buhari Kan Sayar Da Kadarorin Gwamnati Da Aka Kwato Daga 'Barayin Gwamnatin'
- Hukumar EFCC ta gayyaci Ladidi Mohammed, hadimar ministan shari'a kuma antoni janar, Abubakar Malami don amsa tambayoyi kan sayar da wasu kadarorin gwamnati da aka kwato
- EFCC na zargin cewa ba a bi ka'ida ba wurin sayar da kadarorin na biliyoyin naira da aka kwato daga hannun wadanda ake bincika da rashawa amma Ladidi ta ce umurnin minista ta bi
- Wasu takardu sun nuna cewa AGF Malami ya bawa wasu kamfanoni kwangilar kwato kadarorin duba da cewa akwai hukumomin gwamnati za su iya aikin
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi wa Ladidi Mohammed, shugaban sashin kwato kadarorin gwamnati na ma'aikatar shari'ar tambayoyi kan zargin damfara, The Cable ta rahoto.
Da farko, an tsare Ladidi, wacce ta hannun daman Abubakar Malami, ministan shari'a kuma antoni janar ne, na tsawon kwanaki kan zargin damfara wurin sayar da kayayyakin gwamnati na biliyoyin naira da aka kwato daga 'barayin gwamnati.'
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An bada belinta amma bata cika ka'idojin belin ba sai ranar Alhamis.
Amma, majiyoyi sun tabbatarwa The Cable cewa Ladidi ta koma ofishin hukumar a ranar Juma'a domin cigaba da amsa wasu tambayoyin.
An rahoto cewa ta fada wa EFCC ta bi umurnin minista ne wurin sayar da kadarori da gwamnatin tarayya ta kwato hannun mutanen da ake zargi da rashawa.
Sai dai bata iya gabatar da takarda da ke matsayin hujja a hakan ba.
The Cable ta gano cewa ta ce da baki aka bata umurnin.
Karin Haske
Hukumar yaki da rashawa tana bincikar hada-hadar kudi da aka yi da suka shafi Ladidi wacce ake zargi da sayar da kayan a yanayi na zargi
Rahotanni sun ce Malami ya bawa wata kamfani da lauyoyinta kwangilar biliyoyin naira don kwato kadarorin gwamnati.
AGF din ya bawa kamfanin Gerry Ikputu & Partners, masu harkar siyar da fili da gidaje kwangilar kwato kadarori da aka yi imanin na gwamnatin tarayya ne a jihohi 10 da Abuja. Kamfanin ta kuma dauki hayar kamfanin lauyoyi M.E. Sheriff & Co a matsayin wakilinta.
Wasikar Malami na basu kwangilar ta ce za a bashi kashi 3 cikin 100 na dukkan kadarar da aka yi nasarar kwatowa, kuma an yi wata yarjejeniya da ya haramta musu bayyana cikakken bayanin abin da kwangilar ya kunsa.
Wasikar mai dauke da kwanan wata na 5 ga watan Oktoban 2021 ya bawa kamfanin wa'adin wata shida da zai kare a Afrilun 2022.
A kwangilar da M.E. Sherrif & Co, Malami ya ce kamfanin lauyoyin za ta mika kadarorin da ta kwato ga ofishin AGF "don daukan matakan da suka dace."
Kwato kadarori ba hurumin Ma'aikatar Shari'a bane
Masu ruwa da tsaki sun soki AGF da ma'aikatar sharia saboda rawar da suka taka wurin kwato da sayar da kadarorin.
Itse Sagay, shugaban kwamitin bawa shugaban kasa shawarar kan yaki da rashawa, PACAC, ya ce babu wani dalilin daukan hayan kamfanoni masu zaman kansu don kwato kadarorin tunda akwai hukumomin gwamnati na yaki da rashawa da za su iya aikin.
"EFCC da ICPC ne ya kamata su kwato kayan gwamnati da aka sace. Don haka babu dalilin da zai sa a dauki hayan wani ya yi aikin da hukumomin gwamnati za su iya," in ji shi.
EFCC Na Neman 'Babban Yaro' Mompha Ruwa A Jallo, Ta Ta Aika Sako Ga Yan Najeriya
A wani rahoton, hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta ayyana neman dan Najeriya da ya shahara a intanet, Ismaila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, ruwa a jallo.
Hukumar ta EFCC, cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta ta ce duk wani da ke da bayanai masu amfani da za su taimaka a gano inda ya ke ya tuntubi ofishin yan sanda ko EFCC mafi kusa.
Asali: Legit.ng