Da Dumi-Dumi: EFCC Na Neman 'Babban Yaro' Mompha Ruwa A Jallo, Ta Ta Aika Sako Ga Yan Najeriya

Da Dumi-Dumi: EFCC Na Neman 'Babban Yaro' Mompha Ruwa A Jallo, Ta Ta Aika Sako Ga Yan Najeriya

  • Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, EFCC, a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, ta ayyana neman Ismaila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, ruwa a jallo
  • Ana neman dan Najeriyan wanda ya shahara a kafafen sada zumunta ruwa a jallo ne saboda zarginsa da mallakar kudaden da aka samu ta haramtaccen hanya
  • Ana bukatar duk wani wanda ke da bayani kan inda ya ke ya tuntubi ofishin EFCC ko yan sanda mafi kusa da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta ayyana neman dan Najeriya da ya shahara a intanet, Ismaila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, ruwa a jallo.

Mompha
EFCC Na Neman 'Babban Yaro' Mompha Ruwa A Jallo, Ta Ta Aika Sako Ga Yan Najeriya. Hoto: @Mompha_Lifestyle
Asali: Instagram

Hukumar ta EFCC, cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta ta ce duk wani da ke da bayanai masu amfani da za su taimaka a gano inda ya ke ya tuntubi ofishin yan sanda ko EFCC mafi kusa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NBC Ta Ci Aminiya Tarar Naira Miliyan 5 Saboda Bidiyon Tona Asirin Yan Bindiga

Hukumar ta ce "duk wanda ke da bayani mai amfani da zai taimaka a gano inda ya ke ya tuntubi EFCC ko ofishin yan sanda mafi kusa."
"Ana sanar da al'umma cewa Ismaila Mustapha, wanda hotonsa ke sama, Hukumar Yaki Da Rashawa ta EFCC, ne nemansa ruwa a jallo saboda zarginsa da mallakar kudade da aka samu ta haramtattun hanya, mallakar takardu da ke dauke da bayanai na bogi, karya yayin bayyana kadarori da karkatar da abubuwan da aka samu ta haramtattun hanya," EFCC ta rubuta a Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo

A wani rahoton daban, Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na ta ayyana neman Gimba Yau Kumo, surukin Shugaba Muhammadu Buhari ruwa a jallo kan zargin damfara ta $66m, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, Azuka Ogugua, mai magana da yawun hukumar ya ce ana neman Kumo da Tarry Rufus da Bola Ogunsola ruwa a jallo kan zargin ɓannatar da karkatar da kudaden shirin samar da gidaje na ƙasa.

Kumo, tsohon shugaban Bankin Samar da Gidaje na Nigeria, ya auri, Fatima, ƴar shugaban ƙasa a 2016 a Daura, jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel