Bidiyon Amarya Yacine Durkushe A Gaban Iyayen Mijinta Mata Yayin Da Suke Sanya Mata Albarka

Bidiyon Amarya Yacine Durkushe A Gaban Iyayen Mijinta Mata Yayin Da Suke Sanya Mata Albarka

  • An sha shagali kuma kudi ya yi kuka a bikin dan tsohon shugaban kasa, Shehu Yar'adua da amaryarsa Yacine Sheriff
  • An yi shagalin karshe inda iyayen ango, Maryam Abacha, Turai Yar'adua, Amina Namadi Sambo duk suka hadu suka sanyawa amarya albarka
  • An shafe fiye da mako guda ana shagulgulan wannan biki na Shehu da amaryarsa Yacine

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kimanin fiye da mako guda kenan aka shafe ana shagulgulan bikin dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Shehu Yar’adua.

Tun a ranar 23 ga watan Yuli ne aka daura auren Shehu da Amaryarsa Yacine Sherifa a garin Maiduguri da ke jihar Borno.

Sai dai tun daga lokacin ne ake ta liyafa iri-iri kama daga Wushe-wushe, Dina da dai sauransu.

A yanzu kuma an gudanar da liyafar Budan kan amarya inda aka gano iyayen ango mata suna sanyawa amarya albarka.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu

Yacine
Bidiyon Amarya Yacine Durkushe A Gaban Iyayen Mijinta Mata Yayin Da Suke Sanya Mata Albarka Hoto: theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani bidiyo da shafin theweddingstreet_ng ya wallafa a Instagram, an gano Amarya Yacine tsugune a gaban matar tsohon shugaban kasa, Hajiya Maryam Abacha, uwar mjinta, Hajiya Turai Yar’adua, Amina Namadi Sambo da Toyin Saraki.

An jiyo Amina Sambo da Maryam Abacha suna kwararo mata ruwan addu’a kafin daga bisani suka shafe ta da shi tare da yi mata addu’an shiga gidan miji a sa’a.

Daga nan sai uwar mijinta, Hajiya Turai ta dagota daga durkushen da take zuwa kan kujerarta.

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane

A wani labarin kuma, kamar yadda yake kasancewa a tsakanin amare da yan matan amare na wannan zamani, idan aka ce bikin waninsu ya tashi sukan yi shiga ta kece raini.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

Hakazalika, wasu kan yi shiga ta nuna tsaraici duk don nuna cewa sun waye da kuma son ganin hankula sun karkata a kansu.

A wani bidiyo da ya yadu a shafin soshiyal midiya, an gano amaryar sanye da doguwar riga irin na amare sannan kanta lullube da mayafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel