Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sunyi Awon Gaba Da Mutane a Gona
- Yan bingida sun kai hari wani gona da ke karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja sun sace wani direba da yaron motarsa
- Direban da aka ce sunansa Atazamu Azaki da yaron motarsa Ayuba John sun fada hannun yan bindigan ne a lokacin da suka shiga dajin don dako gawayi
- Wani mazaunin unguwar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce daga bisani yan bindigan sun sako yaron motan domin ya tafi gida fadawa iyalan direban su biya kudin fansa
FCT, Abuja - An sake kai hari a karamar hukumar Kwali a Abuja yayin da lamarin tsaro ke cigaba da tabarbarewa a babban birnin tarayyar, Daily Trust ta rahoto.
A kalla sau uku yan bindiga suka kai hari a cikin makon nan a Abuja hakan yasa gwamnatin tarayya ta umurci a rufe FGC, Kwali.
A ranar Lahadi, An sace Mr Sunday Odoma Ojarume da Mrs Janet Odoma Ojarume, a kauyen Sheda a karamar hukumar Kwali, amma daga baya an sako matar mutumin aka ce ta nemo kudin fansa, Daily Trust ta rahoto.
Sheda na da katanga da FGC Kwali, amma an rufe shi bayan sace mata da mijin. Mahukunta makarantar sun tuntubi iyayen yara su taho su kwashe yaran don gudun kada a sace su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jim kadan bayan hakan, gwamnati ta bada umurnin a rufe makarantu a Abuja.
A cewar wani mazaunin garin Chida, Dangana Musa, an sace direba tare da yaron motarsa a harin baya-bayan nan, wanda ya faru a daren Lahadi.
Ya ce sunan direban Atazamu Azaki yaron motarsa Ayuba John, sun tafi dakko gawayi a gona sai yan bindigan suka far musu.
Ya ce masu garkuwan sun taho da manyan bindigu suka tafi da mutanen biyu, daga baya suka sako John ya tafi ya sanar da yan uwansa an sace Azaki.
Martanin yan sanda
Kakakin yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, bata riga ta amsa sakon da aka aike mata ba na neman jin ba'asi game da harin na baya-baya.
Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukuma Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda
A wani rahoton, dan sanda ya riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Jihar Borno, Hon Asheikh Mamman Gadai, hari a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a hanyar Gajiram da Gajiganna lokacin da Asheikh da tawagarsa ke hanyarsu ta zuwa wani aiki, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng