Gwamnatin Buhari na Shirin Kara Haraji, Farashin Yin Waya a Salula Zai Tashi

Gwamnatin Buhari na Shirin Kara Haraji, Farashin Yin Waya a Salula Zai Tashi

  • Gwamnatin Tarayya ta fara yunkurin dabbaka karin haraji a kan kira da sakonnin wayar salula
  • Ministar tattalin arziki ta bayyana haka yayin da Frank Oshanipin ya wakilce ta a wani taro
  • Za a kara harajin da ake biya zuwa 12.5% domin Gwamnati ta rika samun isassun kudin shiga

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kara haraji a kan kudin yin wayar salula da aika sakonni da kuma shiga yanar gizo a Najeriya.

Jaridar nan The Cable ta fitar da wannan rahoto ne a ranar Juma’a 29 ga watan Yuli 2022, inda ta ce Ministar tattalin arziki ta shaida haka a Abuja.

Da ta zanta da masu ruwa da tsaki a wajen wani taro da hukumar NCC ta shirya a makon nan, Zainab Ahmed tace za a amince da karin harajin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Mai arzikin duniya, Jeff Bezos, tare da kyakyawar rabin ransa mai shekaru 52

Wani babban jami’in ma’aikatar tattalin arziki, Frank Oshanipin ya wakilci Ministar wajen taron, ya kuma ce an shirya dabbaka karin da aka yi tuni.

An dawo da batun karin VAT

Oshanipin yake cewa an dakatar da fara amfani da tsarin sabon harajin ne domin gwamnatin tarayya ta bada dama a tattauna da masu ruwa da tsaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministar ta bayyana cewa a halin yanzu kudin da Najeriya ta ke tatsa sun yi kadan, don haka ya zama dole a fara neman hanyoyin samun kudi bayan mai.

Gwamnatin Buhari
Shugaba Buhari a wajen taro Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ya kamata a sake nazari - ATCON

The Guardian tace shugaban kungiyar kamfanonin sadarwa na ATCON watau Ajibola Olude, ya samu yin jawabi a wajen wannan zama da aka yi a jiya.

Mista Ajibola Olude yace ya kamata gwamnati ta duba halin da al’umma suke ciki a irin wannan yanayi, a dakatar da yin wannan kari na kudin waya.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Olude yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne gwamnati ta nemi wasu hanyar kudin, yace kamfanonin ISP na shan wahala saboda karancin kudin waje.

Rahoton da muka samu ya nuna idan aka amince da wannan kari, harajin da gwamnati ke karba ta harkokin sadarwa zai karu zuwa 12.5% kenan.

Kamfanonin sadarwa suna kukan cewa nau’o’in harajin da suke biya sun kai 44. Ita kuwa gwamnati tana ganin kudin shigan da ake samu yayi kadan.

Za ayi fama da yunwa

A cikin makon nan ne rahoto ya zo cewa Majalisar wakilan tarayya ta hango yiwuwar wasu Jihohi su auka cikin matsin yunwa nan gaba kadan.

Kwamitin harkokin noma a majalisar tarayya sun bukaci a fara daukar matakin da ya kamata domin magance barazanar da wasu jihohi 16 suke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel