Hotuna: Mai arzikin duniya, Jeff Bezos, tare da kyakyawar rabin ransa mai shekaru 52

Hotuna: Mai arzikin duniya, Jeff Bezos, tare da kyakyawar rabin ransa mai shekaru 52

  • Hotunan mashahurin mai azrikin duniya, Jeff Bezos, rike da hannun budurwarsa suna tattaki a titin London sun bayyana
  • An ga hamshakin mai kudin sanye da wando da riga masu tsadar £600 inda ita kuwa ke sanye da karamar fara riga
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa, yana soyayya da Sanchez a boye yayin da yake auren MacKenzie Scott wacce suka rabu a farkon 2019

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mamallakin Amazon kuma masahahurin mai arziki, Jeff Bezos, ya bayyana yana tattaki tare da budurwarsa ma'aikaciyar gidan talabijin a London.

An ga Bezos yana tattakawa rike da hannun budurwarsa mai suna Lauren Sanchez mai shekaru 52 a yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Yulin 2022.

Daily Mail ta rahoto cewa, tana sanye da karamar farar riga sanye da wata sarka yayin da shi kuwa ya saka farin wando jeans na Brunello Cucinelli da riga uwan kasa masu darajar Pam 600.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Shugaban Bankin AfDB Da Zukekiyar Matarsa Yayin Da Suka Cika Shekaru 38 Da Aure

Jeff Bezos
Hotuna: Mai arzikin duniya, Jeff Bezos, tare da kyakyawar rabin ransa. Hoto daga dailymail.co.uk
Asali: UGC

Mashahurin 'dan kasuwa wanda ke da kudi darajar £121 biliyan, an gano cewa suna soyayya a sirrance da Sanchez yayin da yake auren MacKenzie Scott mai shekaru 52 wacce ya saka a farkon shekarar 2019.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hotuna: 'Dan Afrika ya kafa tarihin zama mutumin da yafi kowa hangamemen baki a duniya

A wani labari na daban, wani 'dan Afrika ya kafa babban tarihi a duniya bayan ya tabbata mutumin da yafi kowa katon baki a duniya, African Report Files ta ruwaito.

Kamar yadda aka gano, mutumin 'dan asalin kasar Angola kuma hangamemen bakinsa yana daukan gwangwanin kacokan guda daya a bakinsa.

Tuni tarihin duniya ya yadda cewa,, Francisco Domingo Joaquim mai shekaru 28 ya bayyana a matsayin mutumin da yafi kowa katon.

Bakin matashin ya kai girman inci shida da rabi a bude, wangamemen bakin Jacquim na iya daukan gwangwanin lemu mai cin ruwan lemu 330ml baki daya.

Kara karanta wannan

An yi adalci: Mahaifin Hanifa ya yi martani bayan hukunta malamin da ya kashe masa diya

Asali: Legit.ng

Online view pixel